Zagin Annabi a Sokoto: Masu zanga-zanga sun farmaka tare da lalata coci 2 a Sokoto

Zagin Annabi a Sokoto: Masu zanga-zanga sun farmaka tare da lalata coci 2 a Sokoto

  • Bayan kama wasu mutane biyu da ‘yan sanda suka yi da laifin kisan Deborah Samuel, wasu matasa sun gudanar da wata zanga-zanga mai zafi a Sokoto
  • Masu zanga-zangar sun kai hari a wasu coci guda biyu karkashin jagorancin Bishop din darikar Katolika na Sokoto, Matthew Hassan-Kukah
  • Bayan faruwar lamarin, Gwamna Aminu Tambuwal ya kafa dokar hana fita ta sa'o'i 24 a fadin birnin Sokoto

Jihar Sokoto - Wasu matasa masu zanga-zanga a ranar Asabar, 14 ga watan Mayu, sun kona tare da lalata wasu coci biyu karkashin jagorancin Bishop din darikar Katolika na Sokoto, Matthew Hassan-Kukah.

Rabaran Christopher Omotosho, daraktan hulda da jama’a na cocin Katolika na Sokoto ne ya tabbatar da faruwar lamarin, inji rahoton jaridar The Punch.

Matasa sun yi zanga-zanga, sun lalata coci 2 a Sokoto
Zagin Annabi a Sokoto: 'Yan zanga-zanga sun farmaka tare da lalata coci 2 a Sokoto | Hoto: thecable.ng
Asali: Facebook

Omotosho ya bayyana cewa fusatattun matasan sun kona kofar daya daga cikin gine-ginen cocin tare da kona wata mota bas a harabarsa. Ya kara da cewa sun kuma lalata coci na biyu da lamarin ya shafa.

Kara karanta wannan

Dokar kulle: Bishop Kukah ya yabawa matakin Tambuwal, ya karyata batun kai hari gidansa

Rabaran din ya bayyana cewa, ba a samu asarar rai ba yayin hare-haren, in ji TheCable.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Legit.ng ta tattaro cewa sunayen coci biyun da lamarin ya shafa sun hada da Holy Family Cathedral dake kan titin Bello da St Kelvin Gidan Dere, da ke Eastern Bypass na jihar.

Wannan tashin-tashina ya taso ne bayan da wata Deborah dalibar kwalejin ilimi ta Shehu Shagari da ke Sokoto ta yi batanci ga Annabi Muhammad (SAW), laamrin d aya kai ga kashe ta tare da kone gawarta.

Bayan haka rundunar ‘yan sandan ta ce an kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan.

Sai dai a ranar Asabar 14 ga watan Mayu ne daruruwan matasa musulmi dauke da allunan zanga-zanga suka fara mamaye Sokoto inda suka bukaci a sako mutanen biyu.

Masu zanga-zangar sun yi arangama da jami'an tsaro wadanda suka yi harbi domin tarwatsa masu zanga-zangar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ƙungiyar CAN Za Ta Yi Gagarumin Zanga-Zanga Na Ƙasa Kan Kisar Deborah Samuel

An birne Deborah, dalibar da aka kashe kan batanci ga Manzon Allah (SAW)

A wani labarin, an birne Deborah Samuel, dalibar kwalejin ilmin Shehu Shagari da aka kashe a jihar Sokoto kan laifin kalaman batancin ga Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata gareshi).

TheNation ta ruwaito cewa an birne Deborah ne a mahaifarta, Tunga Magajiya, dake karamar hukumar Rijau a jihar Neja.

An birneta misalin karfe 6:30 na yamma a makabartar Kirista dake Tunga Magajiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel