Matasan CAN Sun Bayyana Abin Da Za Su Yi Wa Duk Ɗan Takarar Da Bai Fito Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Deborah Ba

Matasan CAN Sun Bayyana Abin Da Za Su Yi Wa Duk Ɗan Takarar Da Bai Fito Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Deborah Ba

  • Kungiyar Kiristocin Najeriya, reshen matasa ta ce duk dan siyasan da bai fito filli ya yi Alla wadai da kisar Deborah Samuel Yakubu ba, ba zai samu kuri'ansu ba a 2023
  • Kungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar inda ta bukaci jami'an tsaro su dauki matakin hukunta wadanda suka kashe dalibar a Sokoto don gudun tada rikicin addini a kasar
  • YOWICAN ta kuma yi kira ga mambobinta a duk fadin Najeriya da suka cigaba da zaman lafiya su kuma guji daukan doka a hannunsu

Kungiyar Kiristocin Najeriya, reshen matasa (YOWICAN) ta yi barazanar cewa ba za ta zabi duk wani dan siyasa da bai yi alla wadai da kisar da wasu suka yi wa Deborah Yakubu ba kan zarginta da zagin Annabi (SAW), Nigerian Tribune ta rahoto.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi: An Sha 'Zagin' Annabi Lokacin Yana Raye, Amma Bai Kashe Kowa Ba Saboda Hakan

Belusochukwu Enwere, shugaban na YOWICAN na kasa, ya yi kira ga jami'an tsaro su binciko wadanda suka yi kisar da kuma wadanda ke lalata dukiyoyin al'umma a Sokoto yayin zanga-zangar da aka yi na baya-bayan nan don neman sakin wadanda aka kama kan zargin kisa Deborah.

Zagin Annabi: Ba Za Mu Zaɓi Duk Ɗan Siyasan Da Bai Yi Alla Wadai Da Kisan Deborah Ba, Matasan CAN
Zagin Annabi: Ba Za Mu Zaɓi Duk Ɗan Siyasan Da Bai Yi Alla Wadai Da Kisan Deborah Ba, In Ji Matasan CAN. Hoto: Nigerian Tribune/Tekedia.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanarwar ta ce:

"Yau ne rana ta 4 da kisar da wasu musulmi masu tsatsauran ra'ayi suka yi wa Miss Deborah Samuel bayan daukan doka a hannunsu amma mafi yawancin yan siyasan mu da ke neman shugabancin kasa ba su yi tir da abin ko yi wa iyalanta ta'aziyya ba.
"Bayan kashe Deborah, bata gari sun cigaba da lalata kayan mutane, suna kona kayayyakin coci suka zuwa gida-gida suna yi wa kiristoci masu zaune lafiya barazana. Muna kira ga jami'an tsaro su yi abin da ya dace kafin lamarin ya zama yaki na addini.

Kara karanta wannan

'Batanci: Jakadiyar Birtaniya Ta Ce Dole a Hukunta Waɗanda Suka Kashe Ɗalibar Sokoto

"Wannan abin takaici ne da bata rai. Duk dan siyasan da ya ki yi wa kasa ta'aziyya musamman kiristocin kasar a wannan lokacin toh ya manta da batun samun kuri'un mu a 2023. Za mu hada kan mambobin mu a kasa mu tabbatar bai kai labari ba domin shi/ita ba zai yi adalci ba. Najeriya ba kasar addini bace.
"Muna kira ga matasan kiristoci su cigaba da zama lafiya su guji daukan doka a hannu. Tabbas Ubangiji zai yi wa Deborah sakayya. Mutuwarta zai tona asirin masu mugun nufi a Najeriya."

Ƙungiyar CAN Za Ta Yi Gagarumin Zanga-Zanga Na Ƙasa Kan Kisar Deborah Samuel

A wani rahoton, kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, ta bukaci a yi zanga-zanga na kasa bisa kisar da aka yi wa Deborah Samuel, dalibar aji 2 na Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sokoto, rahoton Vanguard.

Shugaban CAN, Rabaran Olasupo Ayokunle, cikin wasikar da ya aike wa dukkan shugabannin kungiyar, ya bukaci kiristoci su yi zanga-zangar lumana a harabar cocinsu a ranar Lahadi 22 ga watan Mayun 2022.

Ya yi kirar ne bayan kisa da kona wata daliba da fusatattun matasa suka yi bayan zarginta da furta kalaman batanci ga Annabi Muhammadu (SAW).

Asali: Legit.ng

Online view pixel