Sojan da aka kama yana sayarwa yan bindiga makamai a Zamfara ya fallasa sunayen wasu Sojoji

Sojan da aka kama yana sayarwa yan bindiga makamai a Zamfara ya fallasa sunayen wasu Sojoji

  • Sojan da aka kama a Zamfara kan zargin yana sayarwa yan bindiga makamai ya buɗe baki, ya faɗi sunayen wasu sojoji biyu da suke aiki tare
  • Hukumar sojojin Najeriya ta damƙe sojan ne mai suna Bala Nura yayin da take bincike kan ɓatan wasu ɗaruruwan Alburusai
  • Sojan ya amsa laifinsa kuma ya yi bayanin yadda suke kasuwanci da yan bindiga da farashin da suke sayarwa

Zamfara - Hukumar sojojin Najeriya ta kama dakarunta guda uku da ke aikin sayarwa yan bindiga makamai a jihar Zamfara, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton cewa a hukumar sojin ta kama wani Soja da zargin sana'ar sayarwa yan ta'addan makamai da kayan sojoji, bayan ya amsa laifinsa, sojan ya faɗi sunayen wasu sojoji da suke aiki tare.

Kara karanta wannan

Cikakken Labari: Wani Bam Ya Tashi a Masallaci Yayin da Mutane ke tsaka da Sallar Jumu'a

Hukumar sojojin Najeriya.
Sojan da aka kama yana sayarwa yan bindiga makamai a Zamfara ya fallasa sunayen wasu Sojoji Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Wata majiyar fasaha ta bayyana cewa an kama sojojin ne yayin bincike kan ɓatan wasu Alburusai sama da 400 a sansanin Sojin FOB dake zaune a Shinkafi, jihar Zamfara.

Sojan da aka kama tun farko mai suna, Bala Nura, da ke aiki da barikin FOB, ya amince yana sayarwa yan ta'adda makamai har ya yi alkwarin sayar da wasu.

Ya ƙara da bayanin cewa yana sayar da Alburusai 100 masu girman 7.62mm kan kudi Naira N100,00. kuma har sun gama cinikin sayar da wasu guda 1,000 a miliyan ɗaya.

Sunayen sojoji biyun da Nura ya fallasa

Bayan asirinsa ya tonu, Nura ya bayana sunayen sojoji biyu, Kofur Ehoda Monday, da kuma Kofur, Shehu Mohammed, waɗan da acewarsa suke sana'ar sayar da makaman tare.

A halin yanzu, hukumomin soji sun ƙara matsa kaimi wajen bincike don ƙara zakulo duk masu hannu a lamarin idan ba su kenan ba.

Kara karanta wannan

Jerin sunayen Jaruman Kannywood da suka fito takara da kujerun da suke nema a 2023

A wani labarin kuma Ɗiyar tsohon ministan Abuja da wasu mutum 11 sun mutu a wani haɗarin jirgin sama a Kamaru

Ɗiyar tsohon ministan Abuja kuma jigo a PDP, Solomon Ewuga, da ke aikin tuƙin jirgin sama ta mutu tare da wasu mutum 11 a haɗarin jirgi.

Bayanai sun nuna cewa Adzuayi Ewuga, ta rasa rayuwarta ne bayan karamin jirgin ya rasa sadarwa da Filin jirgi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel