Sokoto: Bishop Kukah ya yi martani kan kashe dalibar da ta yi batanci ga Annabi
- Jim kadan bayan kashe wata dalibar kwalejin ilimi a jihar Sokoto, Limamin addinin kirista ya yi martani a kai
- Ya yi Allah wadai da lamarin, ya kuma bukaci jami'an tsaro su yi amfani da kwarewa wajen gano wadanda suka yi laifin
- Hakazalika, ya bayyana cewa, wannan bakin aiki bai yi daidai da koyarwar addini ba, inda ya bayyana rashin jin dadinsa
Sokoto - Babban Limamin Cocin Katolika na Diocese na Sokoto, Mathew Kukah, ya yi Allah-wadai da kisan wata dalibar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sokoto a yau Alhamis.
Ya kuma yi kira da a kwantar da hankali kan lamarin, yana mai cewa lamarin ba na addini bane, inji rahoton Channels Tv.
A cewar rundunar ‘yan sanda, an zargi Deborah Samuel, ‘yar matakin karatu na biyu, da yin wani rubutu a dandalin sada zumunta na yanar gizo wanda ya nuna alamun batanci ga manzon Allah (SAW).
Rundunar ‘yan sandan ta ce daliban sun dauki dalibar ne da karfin tsiya daga dakin jami’an tsaro da hukumomin makarantar, suka kashe kana suka kone gawarta.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Legit.ng Hausa ta tattaro daga NewsWire cewa, Kukah ya bayyana maukar fushi yayin da ya ji labarin, kana ya ce:
“Muna Allah-wadai da wannan lamari da kakkausar murya, muna kuma kira ga hukumomi da su binciki wannan mummunan lamari tare da tabbatar da cewa an gurfanar da duk wadanda suka aikata laifin.
“Abin da kawai ya rage wa danginta, abokan karatunta da kuma hukumomin makarantar shi ne tabbatar da cewa duk wanda ya aikata wannan ta’asa, komai jin kansa, anhukunta shi kamar yadda dokokin mu na kasa suka tanada.
"Wannan lamari ba ruwansa da addini. Kiristoci sun zauna lafiya da makwabtansu musulmi a nan Sokoto tsawon shekaru. Dole ne a dauki wannan al'amari a matsayin wani nau'in laifi kuma dole ne doka ta yi aikinta.
“A halin da ake ciki, ina so in yi kira ga daukacin Kiristocin Sokoto da kewaye da su da su kwantar da hankulan su kuma su yi addu’a domin Allah ya jikan Ms Deborah."
Bidiyon kalaman da 'yar kwalejin ilimi a Sokoto tayi ya bayyana, Sarki Musulmi ya yi Allah-wadai
A wani labarin, mai Alfarma Sarkin Musulmi,Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya yi Allah-wadai bisa abinda ya auku a kwalejin ilmin Shehu Shagari dake Sokoto wanda yayi sanadiyar rashin rayuwar daliba.
Masarautar Sarkin Musulmi a jawabin da ta saki tace:
"Masarauta ta samu labarin abin takaicin abubuwan dake faruwa a kwalejin ilmin Shehu Shagari dake Sokoto da ya kai ga mutuwar dalibar makarantar."
Asali: Legit.ng