Bidiyon kalaman da 'yar kwalejin ilimi a Sokoto tayi ya bayyana, Sarki Musulmi ya yi Allah-wadai

Bidiyon kalaman da 'yar kwalejin ilimi a Sokoto tayi ya bayyana, Sarki Musulmi ya yi Allah-wadai

  • Sautin kalaman da Deborah, daliba yar kwalejin ilmin Shehu Shagari dake Sokoto tayi ya bayyana
  • Sarkin Musulmi ya bayyana bacin ransa bisa abinda ya faru a makarantar da ya kai ga rashin rai
  • Jami'an tsaro sun kwamushe mutum biyu da ake zargi da hannu cikin abinda ya faru

Sokoto - Mai Alfarma Sarkin Musulmi,Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya yi Allah-wadai bisa abinda ya auku a kwalejin ilmin Shehu Shagari dake Sokoto wanda yayi sanadiyar rashin rayuwar daliba.

Masarautar Sarkin Musulmi a jawabin da ta saki tace:

"Masarauta ta samu labarin abin takaicin abubuwan dake faruwa a kwalejin ilmin Shehu Shagari dake Sokoto da ya kai ga mutuwar dalibar makarantar."
"Masarauta ta yi Allah-wadai da lamarin gaba daya kuma ta yi kira ga jami'an tsaro su hukunta wadanda suka aikata wannan abu."

Kara karanta wannan

Na rantse babu wanda zai saci ko kwabo idan na zama shugaban kasa, Atiku

"Masarautar na kira ga daukaci jama'ar jihar su zauna lafiya da juna."

Deborah Samuel
Bidiyon kalaman da 'yar kwalejin ilimi a Sokoto tayi ya bayyana, Sarki Musulmi ya yi Allah-wadai Hoto: PremiumTimes
Asali: Twitter

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel