Ma'aurata sun shigar da ƙarar ɗan su gaban Kotu kan ya gaza haifar musu jikoki shekara 6 da masa Aure

Ma'aurata sun shigar da ƙarar ɗan su gaban Kotu kan ya gaza haifar musu jikoki shekara 6 da masa Aure

  • Wani mahaifi da mahaifiyar wani matuƙin jirgin sama sun maka ɗan su gaban Kotu kan yaƙi haihuwa shekara 6 da aure
  • Mahaifan biyu sun bukaci ɗan ya biya su diyyar ɗawainiyar da suka yi da shi ko kuma ya amince ya haifar musu jikan da zasu yi wasa
  • Lauyan iyayen ya tabbatar da cewa Kotun arewacin Indiya zata fara sauraron ƙarar a watan Mayu

India - Wasu iyaye miji da mata sun shigar da ƙarar ɗan su gaban Kotu sun bukaci shi da matarsa su haifar musu jika ko ku su biya dala $650,000.

Mutanen biyu Sanjeev da Sadhana Prasad sun ce sun kashe duk wasu kuɗaɗe da suka yi tanadi wajen tarbiyyartarwa da ilimantar da ɗan su wanda ya zama matukin jirgi, haka nan su suka ɗauki nauyin aurensa.

Kara karanta wannan

Dalibai mata na jami'o'i biyu a Arewa zasu fito tituna zanga-zanga tsirara kan yajin aikin ASUU

Jaridar Channels TV ta ruwaito iyayen matukin jirgin na cewa a halin yanzun kuma suna bukatar ɗan ya sa ka musu da haifo musu jikoki.

Alamar Kotu.
Ma'aurata sun shigar da ƙarar ɗan su gaban Kotu kan ya gaza haifar musu jikoki shekara 6 da masa Aure Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

A ƙorafin da suka rubuta yayin shigar da ƙarar ma'auratan suka ce:

"Ɗan mu ya yi aure tsawon shekara shida kenan, amma har yanzun ba su fara shirin haihuwa ba. Aƙalla idan muna da jikan da zamu yi wasa da shi, zamu jure takaicin da ke damun mu."

Meyasa suka nemi ɗan ya biya wasu kuɗi?

Kuɗin da suka nemi ɗan ya biya rufi miliyam 50 sun ƙunshi kuɗin da suka kashe lokacin auren sa a 5-Star Hotel, sabuwar motar alfarma da suka saya masa kan dala $80,000 da kuma kuɗin yawon shaƙatawar su.

Haka nan iyayen sun sake fitar da dala $65,000 domin ɗan su ya samu horon zama matukin jirgin sama a kasar Amurka, kuma haka ya koma gida Indiya ba tare da aikin yi ba.

Kara karanta wannan

Cikakken Labari: Wani Bam Ya Tashi a Masallaci Yayin da Mutane ke tsaka da Sallar Jumu'a

"Tilas ta sa muka nemi bashi domin gina gidan da muke ciki amma yanzun mun shiga cikin yanayin rashin kuɗaɗe. Ga shi muna zaune mu kaɗai abun duniya ya ishe mu."

Lauyan iyayen mutumin, Arvind Kumar, ya ce za'a fara zaman sauraron ƙarar a Kotun arewacin Indiya a ranar 17 ga watan Mayu.

A wani labarin kuma wata mata ta nemi saki a Kotu, ta ce bisa kuskure tsohon saurayinta ya tura wa mijinta Hotunan tsiraici ya ɗauka ita ce

Wata matar aure ta garzaya Kotu ta nemi a raba ta da mijinta saboda kullum dukanta yake kuma baya sauke nauyin dake kansa.

Matar ta ce ta shiga matasala ne tun lokacin da tsohon saurayinta ya tura wa mijin Hotunan tsiraici ya ɗauka ita ce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel