Tsohon saurayina ya yi kuskuren tura wa Mijina Hotunan tsiraici, Mata ta nemi saki a Kotu

Tsohon saurayina ya yi kuskuren tura wa Mijina Hotunan tsiraici, Mata ta nemi saki a Kotu

  • Wata matar aure ta garzaya Kotu ta nemi a raba ta da mijinta saboda kullum dukanta yake kuma baya sauke nauyin dake kansa
  • Matar ta ce ta shiga matasala ne tun lokacin da tsohon saurayinta ya tura wa mijin Hotunan tsiraici ya ɗauka ita ce
  • Mijin bai sami halartar zaman Kotun ba, Kotu ta ɗage zaman har zuwa ranar 21 ga watan Yuni, 2022

Lagos - Wata mata yar kasuwa, Peace Oyakhilome, ranar Talata, ta shaida wa Kotun Kostamare a Legas yadda Mijinta ya yi fira da tsohon saurayinta, ya nemi ya turo masa hotunan tsiraici kuma ya turo ya ɗauka da ita yake magana.

Daily Trust ta rahoto cewa Matar ta garzaya gaban Kotun ne domin neman a datse igiyoyin auren su saboda yawan dukan da take sha a hannun sa kuma ba ya sauke nauyinsa.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC Ya Sake Janye Takararsa

Kotun Majistire.
Tsohon saurayina ya yi kuskuren tura wa Mijina Hotunan tsiraici, Mata ta nemi saki a Kotu Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Matar ta yi wa Kotu bayanin cewa Mijinta, Jonah Abhumen, ya maida ita jaka kullum duka, kuma ya daina kula da ita da yaran su uku da suka haifa.

Haka nan, Matar ta faɗa wa Kotu cewa Maigidanta ya yi amfani da wayarta ya yi chattin da tsohon suarayinta, ya roki mutumin ya turo hotunan tsiraici, shi kuma ya turo don ya ɗauka da ita suke Chat.

A jawabinta ga Kotu, Peace ta ce:

"Ya dawo gida ya nuna mun Hotunan, ya ɗakko wuka da Bel ya fara dukana, yayin da yake zargi na da cin amanarsa. A ranar Asibiti na kwana sai da na kwashe tsawon wata ɗaya."
"Hawan jini ya kama ni, lokacin da Likita ya gano musabbabin abin da ke jawo mun zuwa Asibiti a kai a kai, sai ya dakatar da mijina daga zuwa Asibitin."

Kara karanta wannan

Na Gaji: Matata Tana Yawan Lakaɗa Min Duka, Maigidanci Ya Roƙi Kotu Ta Raba Aurensu

Matar ta kuma yi ikirarin cewa shaye-shayen mijinta yana taimaka wa wajen narkarta da yake, inda ta ƙara da cewa ba ruwan shi da halin da iyalansa ke ciki.

Wane mataki Kotun ta ɗauka?

Magidancin, Abhumen, bai halarci zaman Kotun ba dan haka Alƙali, Mai Shari'a Adeniyi Koledoye, ya ɗage sauraron ƙarar zuwa 21 ga watan Yuni.

A wani labarin kuma Zaura ya janye daga takarar gwamnan Kano ya koma bayan Gawuna, zai kwace kujerar Shekarau a 2023

AA Zaura, ɗaya daga cikin masu hangen kujerar gwamnan Kano, ya ce ya goyi bayan zaɓin Ganduje na Gawuna/Garo 2023.

Sai dai ɗan siyasan ya ce zai tsaya takarar Sanata mai wakiltar mazaɓar Kano ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262