PDP Ta Zaɓi Sanatan Kaduna Don Ɗare Wa Kujerar Da Abdullahi Ɗanbaba Ya Bari Bayan Komawa APC

PDP Ta Zaɓi Sanatan Kaduna Don Ɗare Wa Kujerar Da Abdullahi Ɗanbaba Ya Bari Bayan Komawa APC

  • Jam'iyyar PDP ta zabi Sanata Danjuma La'ah mai wakiltan Kaduna ta Kudu a matsayin sabon bulaliyar marasa rinjaye a majalisar dattawa
  • An zabi La'ah ne domin dare tsohuwar kujerar ta Sanata Ibrahim Abdullahi Danbaba (Sokoto South) bayan ya koma jam'iyyar APC
  • An karanto wasikar ta nada La'ah ne mai dauke da sa hannun sakataren PDP na kasa, Sanata Samuel Anyawu a fadar majalisar dattawa yayin zaman majalisa

FCT, Abuja - Jam'iyyar PDP ta zabi sanata mai wakiltar Kaduna ta Kudu, Danjuma La'ah a matsayin sabon Mataimakin bulaliyar marasa rinjaye a majalisar Dattawa.

Jaridar The Punch ta rahoto cewa zaben La'ah na kunshe ne cikin wata wasika da aka aike wa shugaban majalisa, Ahmad Lawan kuma aka karanto yayin fara zaman majalisa.

PDP Ta Zaɓi Sanatan Kaduna Don Ɗare Wa Kujerar Da Abdullahi Ɗanbaba Ya Bari Bayan Komawa APC
PDP Ta Zabi Sanatan Kaduna Matsayin Mataimakin Bulaliyar Marasa Rinjaye a Majalisar Dattawa. Hoto: The Punch.
Asali: UGC

Sakataren jam'iyyar PDP na kasa, Sanata Samuel Anyawu ne ya rattaba hannu kan wasikar.

Kara karanta wannan

Kano: Tsohon Kwamishinan Ganduje Ya Fita Daga Jam'iyyar APC

Anyawu ya yi bayani a wasikar cewa an zabi La'ah don maye gurbin da tsohon bulaiyar marasa rinjaye, Sanata Ibrahim Abdullahi Danbaba (Sokoto South) ya bari bayan komawa jam'iyyar APC.

Wasikar ta ce:

"Muna son mu jadada zaben Sanata Danjuma La'ah (Kaduna South) da jam'iyyar PDP ta yi don maye gurbin kujerar mataimakin bulaliyar majalisa na marasa rinjaye.
"Zaben Sanata Danjuma La'ah ya biyo bayan ficewar Sanata Ibrahim Danbaba (Sokoto South) tsohon mataimakin bulaliyar majalisar zuwa APC.
"Da fatan za a bawa Sanata Danjuma La'ah dukkan hadin kai don yin aikinsa, mu huta lafiya."

2023: Tsohuwar Matar Shugaban APC Na Kasa Ta Siya Fom Din Takarar Gwamna a Nasarawa

A wani rahoton, Fatima Abdullahi, tsohuwar matar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, ta siya fom din takarar gwamnan Jihar Nasarawa, The Sun ta rahoto.

Kara karanta wannan

Jiga-jigan APC 10 da ka iya maye gurbin ministocin Buhari masu ficewa

Za ta tsaya takarar ne don a yi zaben fidda gwani na jihar nan da wata daya, The Punch ta ruwaito.

Yayin da ta ke bayani bayan tuntubar shugabannin APC a ofishin jam’iyyar da ke Lafia, ranar Juma’a, Fatima ta ce ta tsaya takarar ne don gyara akan kura-kuran da wannan mulkin ya yi.

A cewarta, Jihar Nasarawa tana bukatar shugaba mai hangen nesa da kuma jajircewa don ciyar da jihar gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel