Da dumi-dumi: Gwamnonin PDP sun shirya ganawar gaggawa gabanin zaben fidda gwani

Da dumi-dumi: Gwamnonin PDP sun shirya ganawar gaggawa gabanin zaben fidda gwani

  • Gabanin taron zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP, jiga-jigan jam'iyyar za su zauna don dinke barakar jam'iyyar
  • Ana sa ran za a yi taron da yammacin yau Laraba bayan dage lokacin yinsa daga karfe 10 na safiyar yau dinnan
  • Rahoton da muka samo ya bayyana sabon jadawalin tarukan da za a yi a lokuta mabambanta a yau Laraba

Abuja - Gwamnonin jam'iyyar PDP sun shirya yin wani taro a wani zama na hadin gwiwa a Abuja gabanin babban taron kwamitin zartarwa na jam'iyyar na kasa a yau.

Taron an ce zai gudana ne a masaukin Gwamnan Jihar Benue da ke Asokoro, inji rahoton Tribune Online.

Tuni dai akasarin shuwagabannin jam’iyyar na jihohi da jiga-jigai suka isa wurin taron wanda aka ce zai gudana da yammacin yau dinnan.

Kara karanta wannan

Rokon da Shugaba Buhari ya yi, ya fada a kan kunnen kashi, ASUU ta cigaba da yajin-aiki

Taron gaggawa ta gwamnonin PDP
Da dumi-dumi: Gwamnonin PDP sun shirya ganawar gaggawa gabanin zaben fidda gwani | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Babban manufar taron dai ana tunanin shi ne batun raba tikitin takarar shugaban kasa na jam'iyyar adawa a zaben 2023 mai cike da takaddama.

Gwamnan da ya karbi bakuncin taron, Samuel Ortom, shi ne shugaban kwamitin shiyya na jam’iyyar PDP, wanda ya kasa cimma matsaya kan lamarin.

PDP ta dage taron da aka shirya yi a yau Laraba

Sai dai, wnai rahoton Vanguard ya ce, shugabancin jam’iyyar PDP ya sauya jadawalin taron na kwamitin amintattu na kasa da na majalisar zartarwa ta kasa ta PDO da aka shirya gudanarwa tun daga karfe 10 na safe zuwa 2:00 na rana.

Amma an yi ganawar bayan labule da fitattun ‘yan jam’iyyar da suka hada da tsaffin shugabannin majalisar dattawa, David Mark da Bukola Saraki, da shugaban BoT Sen. Walid Jibrin.

Kara karanta wannan

2023: PDP Ta Yi Watsi Da Batun Ba Wa Kudu Mulki, Ta Ce Kowa Na Iya Takarar Shugaban Ƙasa

Hakazalika da gwamnonin Edo, Enugu, Adamawa, Taraba mai masaukin baki, Samuel Ortom, da sauran su, kimanin awanni biyu kafin gabatar da shirin taron da misalin karfe 12:00 na rana.

Duk da cewa ba a fitar da wata sanarwa a hukumance ba, Vanguard ta tattaro cewa taron wanda zai dauki tsawon sa'o'i kadan zai bada damar tattaunawa kan batutuwa masu sarkakiya.

A bisa sabon tsarin jadawalin taron, za a fara taron kwamitin da karfe 4:00 na rana, za a yi taron na BoT da karfe 7 na dare yayin da ake shirin gudanar da taron na NEC zai fara da karfe 8:00 na dare.

Na samawa matasa 700 aiki a jihar Kebbi, na sama mutum 6000 tallafin Korona: Abubakar Malami

A wani labarin, Antoni Janar na tarayya kuma dan takaran kujerar gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Malami, ya ce ta dalilinsa mutum sama da 500 sun zama miloniy a jihar.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Hadimin Buhari, Bashir Ahmad ya yi murabus daga kujerarsa

Malami ya bayyana hakan ne gidansa dake Birnin Kebbi yayinda ya karbi bakuncin kungiyar magoya bayansa makon da ya gabata, rahoton PremiumTimes.

Ya kara da cewa ya samawa matasa sama da 700 ayyuka. A cewarsa: "Mun samu nasarar samawa mutum 700 ayyukan yi. Mun gina rijiyar burtatsai sama da 200 a fadin jihar, muna taimakawa jihar wajen mayar da mutane 500 miloniya a jihar."

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.