2023: PDP Ta Yi Watsi Da Batun Ba Wa Kudu Mulki, Ta Ce Kowa Na Iya Takarar Shugaban Ƙasa

2023: PDP Ta Yi Watsi Da Batun Ba Wa Kudu Mulki, Ta Ce Kowa Na Iya Takarar Shugaban Ƙasa

  • Kwamitin zartarwa na jam'iyyar PDP, NEC, ta yi watsi da tsarin karba-karba ta ce kowa zai iya neman takarar shugaban kasa
  • Jam'iyyar ta bayyana hakan ne cikin sakon bayan taronta ta bakin kakakin ta Debo Ologunagba bayan taron na NEC
  • Jam'iyyar ta kuma tabbatar da cewa za ta yi taronta na kasa a babban birnin tarayya, Abuja a karshen watan Mayun 2022

FCT, Abuja - Kwamitin zartarwa, NEC, na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta yanke shawarar bawa kowa fitowa takarar shugaban kasa a maimakon mika mulkin ga yanki guda na kasar, rahoton Premium Times.

Mai magana da yawun PDP, Debo Ologunaba, ya sanar da hakan yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi a sakatariyar jam'iyyar a Abuja.

Kara karanta wannan

Dan Marigayi Abiola Ya Shiga Jerin Masu Son Gaje Kujerar Buhari, Ya Siya Fom Din Takara

2023: PDP Ta Yi Watsi Da Batun Ba Wa Kudu Mulki, Ta Ce Kowa Na Iya Takarar Shugaban Ƙasa
2023: PDP Ta Yi Watsi Da Karba-Karba, Ta Ce Kowa Na Iya Takarar Shugaban Ƙasa. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

NEC din kuma ta kara da cewa jam'iyyar ta yi aiki domin zaben dan takarar shugaban kasa ta hanyar sassanci.

Daily Trust ta rahoto cewa kwamitin karkashin jagorancin Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benue ta bada shawarar cewa duk da cewa karba-karba na kundin tsarin jam'iyyar, a jingine shi a babban zaben 2023.

Da ya ke magana kafin zaben na NEC, Dr Iyorchia Ayu, shugaban jam'iyar na kasa, ya ce NEC din tana aiki tare da rana don daidaita jam'iyyar.

Ya ce:

"Muna kuma aiki domin babban taron mu na kasa, kuma za mu yi muku bayani a nan gaba. Muna son mu mika godiya da wadanda suka yi aiki da su, a kwamitoci daban-daban.
"Yanayin jam'iyyar ya fara canja wa, kowa na aiki tukuru kuma idan muka cigaba haka babu abin da zai hana mu kwace mulki daga jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Bayan An Tara Masa N83m Don Siyan Fom Ɗin Takara, Adamu Garba Ya Fice Daga APC, Ya Bayyana Dalili

"Shugaban kungiyar gwamnonin PDP kuma Gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal ya ce yanzu ma aka fara yi wa jam'iyyar garambawul kuma 'muna tare da kai har zuwa zabe na kasa."

Jonathan Ba Zai Sake Iya Yin Takarar Shugaban Kasa Ba a 2023, Falana Ya Bada Hujja

A bangare guda, Mr Femi Falana, SAN, a jiya Laraba ya ce tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba zai iya yin takarar shugaban kasa ba a zaben 2023, Vanguard ta rahoto.

Lauya mai kare hakkin bil-adama ya ce Jonathan ba zai iya takarar ba saboda sashi na 137 (3) na kundin tsarin mulkin Najeriya ta 1999 (da aka yi wa gyaran fuska) kamar yadda SaharaReporters ta rahoto.

Ana ta hasashen cewa tsohon shugaban kasar zai iya fice wa daga jam'iyyar PDP ya koma APC gabanin zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel