Na samawa matasa 700 aiki a jihar Kebbi, na sama wa mutum 6000 tallafin Korona: Abubakar Malami

Na samawa matasa 700 aiki a jihar Kebbi, na sama wa mutum 6000 tallafin Korona: Abubakar Malami

  • Dan takaran gwamnan Kebbi ya lissafa jerin abubuwan alherin da ya yiwa al'ummar jihar da yake son mulka
  • Abubakar Malami yace yanzu yana kokarin mayar da mutum 500 masu kudi miloniya
  • Malami, wanda shine Ministan Shari'a ya jaddada karyata rahotannin cewa ya rabawa deleget motoci

Birnin-Kebbi - Antoni Janar na tarayya kuma dan takaran kujerar gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Malami, ya ce ta dalilinsa mutum sama da 500 sun zama miloniya a jihar.

Malami ya bayyana hakan ne a gidansa dake Birnin Kebbi yayinda ya karbi bakuncin kungiyar magoya bayansa makon da ya gabata, rahoton PremiumTimes.

Ya kara da cewa ya samawa matasa sama da 700 ayyuka.

A cewarsa:

"Mun samu nasarar samawa mutum 700 ayyukan yi. Mun gina rijiyar burtatsai sama da 200 a fadin jihar, muna taimakawa jihar wajen mayar da mutane 500 miloniya a jihar."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ministan Buhari Da Ya Yi Murabus Don Takarar Gwamna Ya Janye Takararsa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Mun taimakawa sama da mutum 6000 wadanda suka samu tallafin COVID-19 kowanne N550,000."

Abubakar Malami
Na samawa matasa 700 aiki a jihar Kebbi, na sama mutum 6000 tallafin Korona: Abubakar Malami Hoto: Channels Tv
Asali: UGC

Ni 'dan Malamin addini ne, bana neman mulki, sai dai a rokeni in yi : Malami

Abubakar Malami, ya bayyana shirinsa na neman takarar gwamnan Kebbi a babban zaɓen 2023 dake tafe.

TheNation ta rahoto cewa Malami, wanda ya bayyana shirinsa ranar Alhamis, 28 ga watan Afrilu, 2022.

Malami yace ya yanke shawarar takara ne bayan amsa kiran da mutane ke masa na ya zama gwamna.

Malami ya bayyana hakan a jawabin da yayi a Birnin Kebbi yayin tattaunawa da masu ruwa da tsakin jam'iyyar APC, riwayar Tvcnewsng.

Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, a jawabinsa ya yi kira da shugabannin jam'iyyar kada suyi kasa a gwiwa wajen hada kan 'yayan jam'iyya.

Kara karanta wannan

Dan Marigayi Abiola Ya Shiga Jerin Masu Son Gaje Kujerar Buhari, Ya Siya Fom Din Takara

Ya yi kira ga matasa su yi koyi da tawali'un Malami a matsayinsa na dan Malamin addini.

Asali: Legit.ng

Online view pixel