Na Gaji: Matata Tana Yawan Lakaɗa Min Duka, Maigidanci Ya Roƙi Kotu Ta Raba Aurensu

Na Gaji: Matata Tana Yawan Lakaɗa Min Duka, Maigidanci Ya Roƙi Kotu Ta Raba Aurensu

  • Wani manomi, Williams Famuyibo, a ranar Laraba ya bukaci kotu ta raba aurensu mai shekaru 32 akan yadda matarsa ta ke yawan dukansa
  • Famuyibo, wanda mazaunin Ibadan ne ya ce ya gaji da cin bakin-duka a hannun matarsa akan wannan dalilin ne yasa ya taba guduwa daga gidan a watan Janairu
  • Ya bayyana wa kotu yadda tsabar cutarwar da matarsa ta ke yi masa ya sanya shi kwashe ya nashi ya nashi ya koma wurin dan uwansa

Oyo - A ranar Laraba, wani manomi, Williams Famuyibo ya bukaci wata kotun Mapo mai daraja ta daya da ke zama a Ibadan da ta raba aurensu mai shekaru 32 da matarsa akan nada mishi dukan da ta ke yawan yi.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC Ya Sake Janye Takararsa

Ya ce ya gaji da cin duka a hannun matarsa hakan ya sa ya bar gidansa a watan Janairu, Daily Nigerian ta ruwaito.

Na Gaji: Matata Tana Yawan Lakaɗa Min Duka, Maigidanci Ya Roƙi Kotu Ta Raba Aurensu
Matata Tana Yawan Lakaɗa Min Duka, Maigidanci Nemi Raba Shi Da Matarsa. Hoto: Daily Trust.
Asali: UGC

Har yaransa ta ke cutarwa

Ya shaida wa Alkali cewa:

“Mai girma mai shari’a saboda tsabar muguntar da ta ke yi min na koma zama a gidan dan uwana. Na kasa samun natsuwa saboda ba ta iya kulawa da ni.
“Ina da yara kafin in auri Sola a 1990, amma duk yanzu na rarraba su hannun ‘yan uwana saboda tsabar azabtar da su da Sola ta ke yi.”

Sola ba ta je kotun ba

Sai dai bisa ruwayar News Express, Sola ba ta halarci zaman kotun ba sannan ba ta tura lauya ba, duk da an tura mata takardar gayyatar kotu.

Kara karanta wannan

'Batanci: Atiku Ya Ce Ba Shine Ya Wallafa Rubutun Sukar Kashe Ɗalibar Sokoto a Shafinsa Ba

Alkalin kotun, S. M. Akintayo ta bukaci ma’aikaciyar kotun da ta sanar da wacce ake karar ranar da kotu za ta kara zama.

Daga nan Akintayo ta dage sauraron karar zuwa ranar 26 ga watan Mayu don ci gaba da shari’ar.

Ba zan iya ba: Jarabar mijina ta yi yawa, yana so ya kashe ni da saduwa, Matar aure ga kotu

A wani labarin, wata matar aure mai 'ya'ya uku, Olamide Lawal, a ranar Juma'a ta roki kotun Kwastamare da ke zamansa a Mapo, Ibadan, ya raba aure tsakaninta da mijinta, Saheed Lawal, saboda yana jarabar ta da yawan saduwa, rahoton Premium Times.

A karar da ta shigar, Olamide wacce ke zaune a Ibadan ta kuma yi ikirarin cewa mijinta ya saba shan giya ya yi tatil yana maye, The Nation ta ruwaito.

Ta ce:

"Mun shafe shekaru 14 muna zaman aure da Lawal. Tantirin mashayin giya ne kuma ba shi da tausayi ko kadan a zuciyarsa.

Kara karanta wannan

2023: Ministan Buhari ya bayyana abun da zai yi kafin ya bi umurninsa na yin murabus

"Abin da ya mayar da hankali a kai shine shan giya, duka na da kuma tilasta min kwanciyar aure da shi. Baya kulawa da yaran mu.
"Ba zan iya cigaba da zama tare da shi ba."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags:
Online view pixel