Bayan kammala 'Next Level', babban lauya ya nemi a kara wa Buhari wa’adin mulki

Bayan kammala 'Next Level', babban lauya ya nemi a kara wa Buhari wa’adin mulki

  • Har ila yau, wani babban jigo kuma lauya a Najeriya ya yi kira da a soke zaben 2023 da kasar ke shirin yi nan kusa
  • Cif Robert Clarke ya ce kalubalen rashin tsaro da ke kara tabarbarewa a kasar ba ba zai haifar da da mai ido a zaben 2023 ba
  • A bangare guda, ya bayyana cewa wa’adin Buhari zuwa zaben 2023 bai isa a dakile matsalar rashin tsaro a kasar nan ba

Babban Lauya, kuma dattijon kasa, Cif Robert Clarke (SAN), ya yi kira da a kara wa shugaban kasa Muhammadu Buhari wa’adin mulki bayan kammala mulkinsa na biyu a 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Babban lauyan, wanda ya bayyana hakan a ranar Litinin din da ta gabata, ya bayyana cewa watannin da ke gabanin zaben 2023 ba su isa su kawo karshen rashin tsaro ba, balle a iya zabe cikin kwanciyar hankali.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Buhari fa na da dan takarar da yake so ya gaje shi, Adesina ya magantu

An nemi a karawa Buhari wa'adin mulki
Bayan kammala 'Next Level', babban Lauya ya nemi a kara wa Buhari wa’adin mulki | premiumtimesng.com
Asali: UGC

Da yake magana a gidan talabijin na Arise, Clarke ya ci gaba da cewa kundin tsarin mulkin kasar ya tanadi cewa shugaban kasa zai iya tsawaita wa’adinsa na tsawon watanni shida, tun da farko, idan yana jin cewa gudanar da zabe zai iya zuwa da tasgaro.

Ya ce ba daidai ba ne a yi imani cewa Shugaban kasa ba zai iya ci gaba da zama a karagar mulki sama da shekaru takwas na wa’adin mulki biyu ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Clarke ya ce shugaban kasar na iya kara wa kansa wa'adin watanni shida domin gudanar da zabe cikin lumana.

Tsawaita wa’adin mulkin Buhari doka ma ta amince dashi – Cif Clarke

Yayin da yake karin haske kan dalilin da ya sa Buhari ka iya kara wa’adin mulkinsa, dattijon ya bayyana cewa matakin bai sabawa doka ba, domin yana nan a rubuce a kundin tsarin mulkin kasar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Saraki ya bayyana alherin da ya tanadar wa 'yan Najeriya idan ya gaji Buhari

Ya kara da cewa a wani yanayi da shugaban kasar ke ganin ba za a samu kwanciyar hankali ba, yana da damar tsawaita wa'adinsa har na tsawon watanni shida kamar yadda jaridar Tribune Online ta ruwaito.

Shugaban Majalisar Dattawa Lawan ya shiga takarar Shugaban kasa a APC

A wani labarin, a ranar Litinin din nan ne shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan ya shiga jerin masu neman takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC mai mulki.

Jaridar The Nation ta ce, yanzu dai Lawan ya zama dan takara na 24 da ya zabi jam'iyyar tare da nuna sha'awarsa ta sayen fom din tsayawa takara gabanin zaben fidda gwani na ranar 30 ga watan Mayu.

Wata kungiyar abokansa karkashin jagorancin Cif Sam Nkire, dan majalisar jam’iyyar na kasa da wasu Sanatoci 15 ne suka saya masa fom din a dakin taron kasa da kasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Buhari Ya Roƙi ASUU Ta Janye Yajin Aiki, Ya Ba Wa Ɗalibai Haƙuri

Asali: Legit.ng

Online view pixel