Daga karshe: Shugaban Majalisar Dattawa Lawan ya shiga takarar Shugaban kasa a APC

Daga karshe: Shugaban Majalisar Dattawa Lawan ya shiga takarar Shugaban kasa a APC

  • Yayin da ake ci gaba da yada jita-jitar cewa zai fito takara, shugaban majalisar dattawa ya samu fom din tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023
  • A yau ne wasu abokansu suka karba masa fom din tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar APC mai mulki
  • Ya zuwa yanzu dai akwai akalla 'yan takarar shugaban kasa 24 daga jam'iyyar ta APC, lamarin ke kara jan hankalin jama'ar kasar nan

A ranar Litinin din nan ne shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan ya shiga jerin masu neman takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC mai mulki.

Jaridar The Nation ta ce, yanzu dai Lawan ya zama dan takara na 24 da ya zabi jam'iyyar tare da nuna sha'awarsa ta sayen fom din tsayawa takara gabanin zaben fidda gwani na ranar 30 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC Ya Sake Janye Takararsa

Shugaban majalisa zai tsaya takarar shugaban kasa
Daga karshe: Shugaban Majalisar Dattawa Lawan ya shiga takarar Shugaban kasa a APC | Hoto: puncngng.com
Asali: Facebook

Wata kungiyar abokansa karkashin jagorancin Cif Sam Nkire, dan majalisar jam’iyyar na kasa da wasu Sanatoci 15 ne suka saya masa fom din a dakin taron kasa da kasa da ke Abuja.

Sam Nkire, ya shaida wa manema labarai cewa “Ba mu zo nan don kanmu ba, muna da goyon bayansa ne.”

Ya kara da cewa:

“Ko da yake abokai da ’yan’uwa sun ba da gudummawa don siyan masa wannan fom din amma ya ba mu izinin yin hakan.”

2023: Kotu ta ki amincewa gwamnan CBN ya tsaya takara har sai ya bar kujerarsa

A wani labarin na daban kuma, wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ki amincewa da bukatar Gwamnan CBN, Godwin Emefiele na hana INEC da Babban Lauyan Tarayya Abubakar Malami hana shi tsayawa takarar Shugaban kasa a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da yasa Buhari ba zai binciki wadanda ke siyan fom din miliyan N100 ba

Gwamnan babban bankin na CBN a ranar Litinin ya shaidawa kotu a Abuja cewa zai iya tsayawa takarar shugaban kasar tarayyar Najeriya ba tare da ya bar mukaminsa na Gwamnan CBN ba.

Gwamnan babban bankin na CBN ta bakin Lauyan sa Mike Ozekhome, ya shaida wa kotun cewa sashe na 84 ((12) na dokar zabe da aka yi wa gyara na 2022 bai shafe shi ba, kasancewarsa ma’aikacin gwamnati ne ba dan siyasa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel