Tashin hankali: Tsagerun Kudu sun kone mota makare da shanu da ta taso daga Arewa

Tashin hankali: Tsagerun Kudu sun kone mota makare da shanu da ta taso daga Arewa

  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, wasu tsageu sun tare motar jama'ar da suka taso daga jihar Taraba, sun kone ta kurmus
  • Rahoton ya bayyana cewa, an kone shanu, wasu sun tsere daji yayin da mutanen da ke cikin motar suka tsallake rijiya da baya
  • Lamarin da bai kasance na farko ba, an sha samun irin wannan barna daga 'yan ta'adda a yakin Kudu maso Gabashin Najeriya

Anambra - Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan wata mota makare da shanu akan titin Ezinifitte/Uga a karamar hukumar Aguata ta jihar Anambra.

Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Lahadi, inji rahoton jaridar Punch.

A cewar wata majiya, motar tana kan hanyarta ta zuwa wata kasuwa a jihar ne, inda aka samu akasi ‘yan bindigar suka kai hari tare da kona ta.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja

Barnar 'yan IPOB a Anambra
Tashin hankali yayin da 'yan ta'adda suka koma kona mota makare da shanu daga Arewa | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Duk da cewa ba a samu asarar rai ba, wani ganau ya bayyana cewa wasu daga cikin mutanen da ke cikin motar sun samu raunuka, inji rahoton The Nation.

Wani faifan bidiyo na lamarin da aka gani a kafafen sanda ya nuna yadda wasu shanun suka watse daga hanyar zuwa cikin dazukan da ke kewaye.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce:

“Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta ceto wani Mohammed Lawan na jihar Taraba tare da dawo da dabbobi 34 a hanyar Ezinifite da Uga a karamar hukumar Aguata. An yi aikin ceton ne biyo bayan kiran gaggawa da aka yi a yau, 8 ga watan Mayu, da misalin karfe 8 na safe, na kone-kone da kuma cin zarafin dabbobi da ‘yan bindiga suka yi.

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi

“Bayanin farko sun nuna cewa wadanda abin ya shafa na kan hanyar wucewa ne, suna jigilar dabbobi zuwa Awarasi, karamar hukumar Uga Aguata. A halin yanzu dai jami’an ‘yan sanda na can a yankin kuma an kwantar da tarzomar.”

Zamu hana kai Shanu jihar Legas, dss: Gwamnatin jihar Adamawa

A wani labarin, gwamnatin jihar Adamawa ta yanke shawarar hana kai Shanu yankunan kudu saboda toshe yoyon kudaden shiga da kuma ingantashi ta hanyar kaiwa wasu jihohi.

Sakataren gwamnatin jihar, Bashir Ahmad, ya yi bayanin wannan sabuwar dokar.

Yace gwamnatin jihar ta yanke shawarar hana kai Shanu wasu jihohin kudu cikin har da Legas saboda suna karban harajin N35,000 kan shanu guda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.