Kano: Kotu ta yanke a rataye matashi mai shekaru 19 bisa laifin sacewa da kashe dan yayarsa

Kano: Kotu ta yanke a rataye matashi mai shekaru 19 bisa laifin sacewa da kashe dan yayarsa

  • Rahoton da ke iso mu daga jihar Kano ya bayyana cewa, an yankewa wani matashi hukuncin kisa ta hanyar rataya
  • Wannan na zuwa ne bayan da kotu ta gamsu da hujjojin da masu gabatar da kara suka bayyana a gabanta
  • A baya an kawo rahoton yadda wani matashi ya shake dan 'yar uwarsa uwarsa da leda har ya mutu a shekarar 2019

Kano - Wata babbar kotu a Kano a ranar Litinin ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wani matashi mai shekaru 19 Ibrahim Khalil, bisa samunsa da laifin yin garkuwa da dan 'yar uwansa, Ahmad Ado mai shekaru biyar, tare da haddasa mutuwarsa.

Khalil, wanda ba a bayyana adireshinsa ba, an yanke masa hukunci ne kan tuhume-tuhume biyu da suka hada da yin garkuwa da kuma laifin kashe yaro ta hanyar shake shi da leda, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja

Yadda aka yankewa matashi hukuncin kisa a Kano
Kotu ta yanke wa matashi hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin sace 'yar yayansa | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Twitter

Alkalin kotun, Mai shari’a Usman Na’abba, ya bayyana cewa masu gabatar da kara sun tabbatar da tuhumarsa ba tare da wata shakka ba, sannan ta yanke wa wanda ake tuhuma hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari bisa samunsa da laifin satar mutane.

Na’abba ya kuma yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kisan kai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tun da farko, Lauyan masu gabatar da kara, Mista Lamido Sorondinki, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhumar ya aikata laifin ne a wani lokaci a shekarar 2019 a unguwar Karkasara a jihar Kano.

A cewarsa:

“Wanda ake tuhumar ya yi garkuwa da dan ‘yar uwarsa, Ado kuma a kan haka ne ya yi amfani da wata leda ya rufe masa hanci da baki wanda hakan ya sa ya shide har ya mutu.
“Ya binne shi a wani rami mara zurfi a Sabuwar Sheka Kano.”

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa ya rigamu gidan gaskiya

Mai gabatar da kara ya gabatar da shaidu uku a gaban kotun tare da gabatar da hujjoji hudu da suka tabbatar da tuhumar da ake yi wa wanda ake tuhuma.

Sai dai mai laifin ya musanta aikata laifin.

A cewar mai gabatar da kara, laifin ya ci karo da sashe na 274 da 221 (a) na kundin laifuffuka da hukunci.

Hanifa: Abdulmalik Tanko ya yarda da sace ta, ya karyata batun kashe yarinyar

A wani labarin, Abdulmalik Tanko, malamin makaranta da ake zargi da sace dalibarsa mai shekaru 5, Hanifa Abubakar, da kuma ya kashe ta, ya sake musanta batun sanin yadda aka yi yarinyar ta mutu.

Ya karyata batun ne a babbar kotu mai lamba ta 5, da ke zama a Audu Bako a ranar Litinin, 9 ga watan Mayu, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Mai shari’a Usman Na’abba ne ya jagoranci zaman kotun. Tanko, wanda a baya ya amince da hada baki da wasu wajen aikata laifin, ya musanta sauran tuhume-tuhume uku da ake masa da su da suka hada da yin garkuwa da yarinyar da kuma kashe ta daga baya.

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi

Asali: Legit.ng

Online view pixel