Rikicin APC a Kano: Daraktan kamfen din Tinubu ya yarda a yi sulhu, watakila ya sake dawowa APC

Rikicin APC a Kano: Daraktan kamfen din Tinubu ya yarda a yi sulhu, watakila ya sake dawowa APC

  • Yayin da rikicin siyasar Kano ke kara daukar wani salo, daraktan kungiyar kamfen din Tinubu ya bayyana ficewarsa daga APC
  • Sai dai, gwamna Ganduje ya shiga tsakani, ya ce mazabar da ke da matsala ta gaggauta dinke barakar da ke tsakani
  • Ya zuwa yanzu dai Jibrin Kofa ya bayyana amincewarsa da zaman tattaunawa domin shawo kan matsalar

Kano - A jiya ne daraktan kamfen din takarar shugaban kasa na Bola Ahmed Asiwaju Tinubu, Abdulmumini Jibrin Kofa ya amince da shirin sulhu da gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya gabatar.

A kwanakin baya ne Jibrin ya bayyana ficewa daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar NNPP mai kayan marmari, sakamakon rikicin zaben neman kujerar majalisar wakilai na 2023 ta mazabar Kiru/Bebeji, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Tinubu ya samu 'delegate' 370, ya mika fom dinsa na takarar gaje Buhari

Rikicin APC a Kano: Jibrin ya amince a yi sulhu
Rikicin siyasa: Shugaban kamfen din Tinubu ya yarda a yi sulhu, watakila ya sake dawowa APC | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Gwamna Ganduje, ya umarci sakatariyar jam’iyyar APC ta jihar da ta gaggauta daukar matakai na warware sabanin da ke faruwa a cikin gida da ke tasowa daga masu sha’awar tsayawa takara a mazabar Kiru/Bebeji ta tarayya.

Don haka, nan take sakatariyar jam’iyyar ta bi umarnin ta kuma kira taron masu ruwa da tsaki domin tattauna lamarin a mazabar.

A bisa umarnin gwamnan, shugaban jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Abdullahi Abbas, ya aike da goron gayyata ga masu neman mukamin.

Ya kuma yi kira ga bangarorin da ke rikici da juna da su kwantar da hankula tare da ba jam’iyyar hadin kai da nufin magance rikicin a cikin gida.

Ya ce ganawar za ta fito da matsaya da dukkan masu son tsayawa takarar za su amince da ita.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya karbi Fom din takara kujerar Sanata

An tattaro cewa Abdulmumini Jibrin Kofa ya amince da sulhun jiya a taron da aka yi a bisa umarnin gwamnan.

Kofa wanda ya amince da yunkurin sulhun da aka shirya gudanarwa a ranar Lahadi, ya ce, "A shirye nake a yi zaman tattaunawa", inji Daily Post.

Rikicin APC a Kano: Ganduje na yunkurin hana Jibrin ficewa daga jam’iyyar

A tun farko, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, na kokarin hana tsohon dan majalisar wakilai, Abdulmumin Jibrin, ficewa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

A ranar Asabar ne Jibrin ya ce zai sanar da sabuwar jam’iyyarsa, yana mai cewa ya yi iya bakin kokarinsa ga APC.

Tsohon dan majalisar shine darakta janar na kungiyar kamfen din Bola Tinubu.

A cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, Abdullahi Abbas, Shugaban APC, ya ce Ganduje ya bukaci a magance rikicin da ke tsakanin masu neman wakiltan mazabar Kiru/Bebeji a majalisar wakilai. The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Billahil lazi la ilaha illahuwa za mu rike maka amanarka – Gawuna ga Ganduje

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.