Badakalar Abacha: Burtaniya ta bankado wasu $23.5m da ke alaka da tsohon shugaban Najeriya

Badakalar Abacha: Burtaniya ta bankado wasu $23.5m da ke alaka da tsohon shugaban Najeriya

  • Burtaniya na ci gaba da bankado almundahanar Marigayi Janar Sani Abacha daga satar dukiyar jama'a da ake zargin ya yi
  • A kwanan nan ne Hukumar Kula da Laifukan Kasa ta Burtaniya (NCA) ta bankado sama da dala miliyan 23 na sata
  • Hukumar ta NCA ta sha alwashin cewa Birtaniya ba za ta kasance mafakar masu wawure dukiyar kasa ba, domin za ta ci gaba da gudanar da bincike don bankado kudaden da aka sace

Burtaniya - Rahotanni da ke fitowa sun tabbatar da bankado dala miliyan 23.5 na kudaden da tsohon shugaban kasar Najeriya Marigayi Janar Sani Abacha ake zargin ya sace, inji rahoton PremiumTimes.

Sanarwar bankadar ta fito ne a cikin wata sanarwa da aka buga a shafin yanar gizon Hukumar Kula da Laifukan Kasa ta Burtaniya (NCA) a ranar Alhamis, 5 ga Mayu.

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi

Badakalar Abacha
Rashawa: Burtaniya ta bankado wasu $23.5m da ke alaka da tsohon shugaban Najeriya Abacha | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Legit.ng ta tattaro cewa dala miliyan 23.5 da hukumar NCA ta bankado ya hada da wawurar kudaden da ma’aikatar shari’a ta Amurka (USDOJ) ta gano wadanda ake kyautata zaton na marigayin ne tare da mukarrabansa.

Kamar yadda ake ci gaba da tattarowa, an bayyana cewa bisa bukatar USDOJ, NCA ta fara binciken tsawan shekaru bakwai da kuma tattaunawa ta kasa da kasa domin samun odar dawo da kudaden.

Bayan cika wasu ka'idojin kasa da kasa, yanzu an tura kudin zuwa Ofishin Cikin Gida don ci gaba da aikawa dasu zuwa USDOJ.

Burtaniya ba za ta zama mafaka ga masu wawure dukiyar jama'a ba - NCA

A cewar Babban Manajan Kadarori na NCA, Billy Beattie, ya ce an yi duk wani yunkuri na dakile duk wani yunkuri na mayar da kasar Burtaniya mafaka ga safarar kudaden haram.

Kara karanta wannan

Sokoto: Bishop Kukah ya yi martani kan kashe dalibar da ta yi batanci ga Annabi

Yace:

"Muna aiki kafada da kafada da Burtaniya da abokan huldar kasa da kasa don tinkarar barazanar da cin hanci da rashawa ke haifarwa, wanda ke illa ga matalautan al'umma da kuma marasa galihu.
"Mun himmatu wajen tabbatar da cewa wadanda ke ci gaba da cin hanci da rashawa ba su amfana da ayyukansu ba."

Ana ci gaba da gudanar da shari’ar NCA inda USDOJ ta gano cewa Abacha da mukarrabansa sun karkatar da wasu kudade.

Badakalar Abacha: Amurka za ta dawowa Najeriya da $400m - ICPC

A wani labarin na daban, Najeriya na sauraron da dawowa Najeriya da kudi dala milyan dari hudu wanda yake kimanin N146bn da tsohon shugaban kasa Sani Abacha ya boye a kasar Amurka lokacin mulkinsa.

Shugaban hukumar yaki da rashawa ICPC, Bolaji Owosanoye ya bayyana hakan ne a taron kungiyar lauyoyin kasar wajen da ya gudana ranar Laraba, 13 ga Nuwamba a Legas.

Kara karanta wannan

Sokoto: An kama wadanda suka kashe dalibar da ake zargin ta zagi Annabi

Owosanoye yace: "A yanzu haka Najeriya na sauraron dawo da kimanin $400 million daga Amurka, wani sashe daga cikin badakalar Abacha."

Asali: Legit.ng

Online view pixel