Badakalar Abacha: Amurka za ta dawowa Najeriya da $400m - ICPC

Badakalar Abacha: Amurka za ta dawowa Najeriya da $400m - ICPC

Najeriya na sauraron da dawowa Najeriya da kudi dala milyan dari hudu wanda yake kimanin N146bn da tsohon shugaban kasa Sani Abacha ya boye a kasar Amurka lokacin mulkinsa.

Shugaban hukumar yaki da rashawa ICPC, Bolaji Owosanoye ya bayyana hakan ne a taron kungiyar lauyoyin kasar wajen da ya gudana ranar Laraba, 13 ga Nuwamba a Legas.

Owosanoye yace: "A yanzu haka Najeriya na sauraron dawo da kimanin $400 million daga Amurka, wani sashe daga cikin badakalar Abacha."

"Mun dawo da $322 million daga kasar Swizalan shekaru biyu da suka gabata daga cikin badakalar Abacha, kuma an yi amfani da wasu wajen shirin CCT.(Biyan talaka dubu biyar-biyar)"

"Hakazalika mun kwato $73 million daga kasar Ingila, wanda aka ajiye a kasar a cinikin mai na Malabu."

KU KARANTA: Faston da matar aure ta yiwa tuhumar fyade: Kotu ta yi watsi da karar, har an ci ta taran N1m

Ya bayyana cewa wasu kasashen basu da niyya dawowa Najeriya da kudinta. Wasu da suka bayyana niyyar dawo da su, suna son a basu wani sashe daga ciki.

Ya bada misali da kasar Ingila inda suka cire $12 million da sunan kudin ajiya.

Ministan shari’a na Najeriya, Abubakar Malami ya bukaci majalisar tarayya da ta aminta cewa ofishinsa ya karba kashi 2.5 na kudin Abacha.

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da gurfana a gaban kwamitin majalisar na shari’a, kare hakkin dan adam da lamurran shari’a don kare kasafin kudi shekarar 2020 na ma’aikatarsa.

“A hankali muke ta samu kudadenmu da aka handame aka adana a kasar waje. Inaso in tabbatar muku da cewa, duk wasu hanyoyi da shari’a ta tanadar don karbo kudaden suna da wuya kuma da yawa,” in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel