Karin bayani: Shugaba Buhari ya dura Enugu, zai zarce Ebonyi ziyarar aiki ta kwana biyu

Karin bayani: Shugaba Buhari ya dura Enugu, zai zarce Ebonyi ziyarar aiki ta kwana biyu

  • A yau ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyarar aiki zuwa jihar Ebonyi, inda ya fara dura a jihar Enugu
  • Rahoton da muke samu daga tushe ya bayyana cewa, shugaban zai shafe kwanaki biyu a jihar domin kaddamar da wasu ayyuka
  • Shugaba Buhari dai na ci gaba da ziyartar jihohin APC domin kaddamar da ayyukan da gwamnoni ke yi

Enugu - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka a filin jirgin sama na Alamo Ibiam na jihar Enugu, inda zai zarce zuwa jihar Ebonyi.

Jirgin shugaban kasar ya isa Enugu ne da misalin karfe 10:30 na dare, The Nation ta ruwaito.

Gwamnan Enugu Ifeanyi Ugwuanyi da takwaransa na Ebonyi David Umahi da sauran jami’an gwamnati sun tarbe shi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa ya rigamu gidan gaskiya

Buhari ya kai ziyara Ebonyi
Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya dura Enugu, zai zarce Ebonyi ziyarar aiki ta kwana biyu | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Shugaban ya kai ziyarar aiki ne ta kwanaki biyu a jihar Ebonyi inda ake sa ran zai kaddamar da ayyuka da dama da gwamnatin Umahi ta aiwatar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An kuma bukaci ya yi gana da zababbun shugabannin yankin Kudu maso Gabas.

Duk da cewa ba a bayyana manufar ganawar ba, ana sa ran cewa matsalolin tsaro a yankin da kuma tsare shugaban IPOB), Nnamdi Kanu ne za su kasance kan gaba a kan batutuwan da za a tattauna.

Wata majiya ta ce wani bangare na abin da shugabannin Igbo za su gabatar wa shugaban a yayin ganawar shi ne yunkurin da yankin ke yi na samar da wanda zai gaje shi a 2023.

Domin tabbatar da cewa yankin na magana da murya daya, an kira taron Imeobi Ohanaeze Ndigbo a Enugu da yammacin ranar Alhamis a sakatariyar kungiyar, inji rahoton The Guardian.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Buhari fa na da dan takarar da yake so ya gaje shi, Adesina ya magantu

Gwarzon Dimokradiyya: Za a karrama shugaba Buhari da babbar lambar yabo

A wani labarin, nan ba da jimawa ba za a karrama shugaban kasa Muhammadu Buhari da lambar yabo ta gwarzon dimokuradiyya, wanda majalisar ba da shawara ta jam’iyyu (IPAC) za ta ba shi.

Jaridar PM News ta ruwaito cewa, Engr. Yusuf Yabagi, shugaban jam'iyyar ADP kuma kodinetan IPAC ne ya sanar da hakan a ranar Talata 26 ga watan Afrilu yayin wata liyafar buda baki da Buhari a Abuja.

Yabagi ya ce za a karrama Buhari ne saboda sanya hannu a kan dokar zabe mai dumbun tarihi domin tana wakiltar sauyi da zai tabbatar da zaman lafiya da karbuwa da zabuka a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.