Jami'an JTF sun kashe ‘yan bindiga 10, sun ceto mutane 14 da aka sace a Neja
- Jami'an tsaro a jihar Neja sun yi nasarar kashe wasu miyagun 'yan bindiga a wani yankin jihar cikin makonnan
- Hakazalika, rundunar ta kwato makamai da babura daga hannun 'yan bindigan bayan ceto wasu mutane da aka sace
- Rahoton da ke iso mu ya kuma bayyana cewa, an kama wasu mafarauta da ke sace shanun da aka kwato daga hannun 'yan bindiga
Jihar Neja Rundunar hadin gwiwa ta jami’an tsaro ta kashe ‘yan bindiga 10 a jihar Neja. Hakazalika, sun kuma ceto mutane 14 da aka yi garkuwa da su a yayin aikin tare kwato babura da makamai daga hannun 'yan ta'addan.
Lamarin ya faru ne a kauyen Uregi da ke karamar hukumar Rafi a ranar Litinin, Vanguard ta ruwaito.
Kwamishinan Kananan Hukumomi da Tsaron Cikin Gida na Jihar, Emmanuel Umar, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce manufar ‘yan bindigar ita ce su tayar da tarzoma a lokutan bukukuwan Sallah kafin su hadu da gamunsu.
Jaridar Daily Sun ta ruwaito kwamishinan na cewa:
“A ranar 02/05/2022 karfe 1700 ne wasu ‘yan bindiga dauke da makamai a kan babura suka yi yunkurin kai hari a kauyukan Kawo, Uregi da ke karamar hukumar Rafi domin dagula bukukuwan Sallah a jihar.
“Bayan samun labarin, rundunar hadin gwiwa ta jami’an tsaro sun mayar da martani cikin gaggawa, inda suka garzaya yankin da ‘yan ta’addan ke kai hare-hare a kauyukan Uregi, Kiribo.
"A sakamakon haka, an kashe ‘yan bindiga 10, an kubutar da mutane 14 da aka yi garkuwa da su, an kuma kwato babura bakwai ciki har da makamai duk dai an kwace daga gare su.”
An kama mafarauta da ke sace shanun da aka kwato daga hannun barayi
A bangare guda kuma, an kama wasu mafarauta da ke barna a karamar hukumar Shiroro ta jihar bisa zargin satar shanu da aka kwato daga hannun ‘yan ta'adda.
Mafarautan dai an dauke su ne domin su tallafa wajen kawo karshen 'yan bindiga a yankin, amma suka sauya daga manufarsu.
Wata majiya daga yankin ta shaida cewa wasu daga cikin shanun da aka kwato daga hannun ‘yan ta'addan makonnin da suka gabata sun bace daga inda aka ajiye su.
Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa wasu daga cikin mafarautan ne suka sace shanun da suka bace.
'Yan ta'addan ISWAP na can suna barna a garin Chibok, sun kori sojoji
A wani labarin, Kautukari da ke karamar hukumar Chibok ta jihar Borno a halin yanzu na fuskantar harI daga wasu da ake zargin mayakan kungiyar ISWAP.
Wani mazaunin garin ya shaidawa TheCable cewa ‘yan ta’addan sun mamaye al’ummar ne da misalin karfe 6 na yammacin ranar Talata inda suka fara harbe-harbe ba kakkautawa. #
Rahotanni sun ce mayakan na ISWAP sun kona gidaje yayin da mazauna yankin ke tserewa cikin daji domin tsira da rayukansu.
Asali: Legit.ng