Shugaba Buhari: Abin da yasa gwamnati na ta gagara yakar 'yan bindiga
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana dalilin da yasa gwamnatinsa ke shan wahala wajen yakar 'yan bindiga
- Shugaban ya bayyana cewa, 'yan ta'adda ba kamar sauran sojoji bane, suna iya take doka da ka'idar yaki
- Ya kuma tabbatarwa 'yan Najeriya cewa, zai tabbatar da tsaron kasa da rayukan 'yan Najeriya a mulkinsa
Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya ce abu ne mai wahala a murkushe ‘yan bindiga saboda yadda ake garkuwa da mutane a matsayin wata garkuwa.
Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin wasu mazauna babban birnin tarayya Abuja a wajen bikin karamar Sallah a fadar gwamnati da ke Abuja, Daily Trust ta ruwaito.
Ya kuma yi magana kan harin jirgin kasa da aka kai a jihar Kaduna, inda ya umurci hukumomin tsaro da su tabbatar da ceto wadanda lamarin ya rutsa da su.
A ranar 28 ga watan Maris ne ‘yan ta’adda suka kai hari kan wani jirgin da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna, inda suka kashe akalla mutane tara tare da raunata wasu da dama, da kuma yin awon gaba da fasinjojin da ba a san adadinsu ba.
Shugaba Buhari, wanda ya tabbatar da cewa, ana ci gaba da kokarin ganin an dawo da duk wadanda ‘yan ta’adda ke tsare da su lafiya, ya ce gwamnati za ta binciko duk wata dama da za ta samu wajen ganin an ceto wadanda ake garkuwa da su, a raye.
Ya umurci hukumar kula da layin dogo ta Najeriya (NRC) da ta samar da karin bayanai na yau da kullum ga iyalan wadanda aka sacen.
A cewar Shugaban, ‘yan bindiga da ‘yan ta’addan ba kamar kwararrun sojoji bane, ba sa mutunta ka’idojin yaki kuma suna iya illata wadanda suka yi garkuwa da su idan aka kai musu hari.
Shugaba Buhari ya bukaci ‘yan Najeriya da su samar da yanayi na kyama ga 'yan ta'adda dake boye a cikin al’umma.
Shugaban ya ce hada karfi da karfe tsakanin jami’an tsaro da al’ummomi ne zai kawo gagarumin sauyi wajen murkushe ‘yan ta'adda da ta’addanci a kasar.
Wankan Sallah: Hotunan Buhari, mukarrabansa da danginsa a ranar karamar sallah
A bangare guda, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bi sahun sauran musulmi a Najeriya, ya harkaci sallar idi a babban birnin tarayya Abuja.
Wata sanarwar da hadimin shugaban kasa, Buhari Sallau ya fitar ta shafin Facebook ta nuna hotunan shugaban lokacin da ya halarci sallar a barikin Mabila da ke Abuja a yau Litinin, 2 ga watan Mayu.
Hotunan sun nuna shugaban cikin farin ciki, yana daga wa jama'a hannu.
Wani yankin sanarwar ya ce:
"Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci Sallar Eid Al-Fitr a barikin Mambila, Abuja ranar 2 ga Mayu, 2022."
Sojoji sun kashe kwamandan ISWAP, sun ceto mutane 848 da aka sace
A wani labarin, Hedikwatar tsaron Najeriya a ranar Alhamis ta sanar da cewa, a kalla mutane 848 da aka yi garkuwa da su ne sojoji suka kubutar a wani samame daban-daban a fadin kasar cikin makwanni uku da suka gabata.
Jaridar Punch ta rahoto cewa, da yake jawabi yayin wani taron manema labarai a Abuja, Daraktan ayyukan yada labarai na tsaro, Janar Benard Onyeuko, ya kuma ce sojoji sun kashe wani fitaccen kwamandan kungiyar ISWAP, Abubakar Dan-Buduma.
Ya kara da cewa an kuma kama masu kwarmato bayanai na ‘yan ta’addan a ayyuka daban-daban tsakanin 7 da 28 ga Afrilu, 2022.
Asali: Legit.ng