Wankan Sallah: Hotunan Buhari, mukarrabansa da danginsa a ranar karamar sallah

Wankan Sallah: Hotunan Buhari, mukarrabansa da danginsa a ranar karamar sallah

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci filin idin barikin Mambila a babban birnin tarayya Abuja
  • Shugaban dai ya bi sahun sauran musulmin Najeriya ne wajen gudanar idin karamar sallah ta shekarar 2022
  • Hotuna sun nuna shugaban tare da danginsa, iyalansa da wasu mukarrabansa jim kadan bayan idar da sallar

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bi sahun sauran musulmi a Najeriya, ya harkaci sallar idi a babban birnin tarayya Abuja.

Wata sanarwar da hadimin shugaban kasa, Buhari Sallau ya fitar ta shafin Facebook ta nuna hotunan shugaban lokacin da ya halarci sallar a barikin Mabila da ke Abuja a yau Litinin, 2 ga watan Mayu.

Hotunan sun nuna shugaban cikin farin ciki, yana daga wa jama'a hannu.

Kara karanta wannan

'Batanci: Bayan Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Deborah a Sokoto, Osinbajo Ya Yi Magana Da Kakkausar Murya

Buhari a sallar idi
Wankan Sallah: Hotunan Buhari da dangi a ranar karamar sallah | Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Wani yankin sanarwar ya ce:

"Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci Sallar Eid Al-Fitr a barikin Mambila, Abuja ranar 2 ga Mayu, 2022."

Hakazalika, sanarwar ta kuma nuno shugaban tare da danginsa; a fadar shugaban kasa bayan dawowarsu daga sallar idin da aka gudanar yau.

Sanarwar ta ce:

"Shugaba Buhari tare da uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari da wasu 'ya'yansu, jikoki, da 'yan uwansu bayan halartar Sallar Idin Sallah a barikin Mambila, Abuja ranar 2 ga Mayu, 2022."

Baya ga ganawa da daniginsa bayan sallar, shugaban ya kuma gaisa da wasu mukarabbansa da jiga-jigan gwamnatin Najeriya.

A cewar Buhari Sallau:

"Shugaba Buhari tare da wasu mukarrabansa bayan halartar Sallar Eid Al-Fitr a barikin Mambila, Abuja ranar 2 ga Mayu, 2022."

Kalli hotunan a kasa:

Shirin 2023: Yahaya Bello ya gana da Buhari domin nuna masa fom din takarar shugaban kasa

Kara karanta wannan

2023: Jerin ministocin da suka yi murabus bayan umurnin Shugaba Buhari

A wani labarin na daban kun ji cewa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari karbi bakuncin gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello a fadarsa da ke Aso Rock Villa da ke Abuja.

Ganawar tasu ta zo ne daidai lokacin da gwamnan ya sayi fom din tsayawa takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC mai mulki gabanin zaben fidda gwani.

Fadar shugaban kasa ta ce, gwamnan ya gana da Buhari a yau Alhamis 28 ga watan Afrilu, kamar yadda hadimin shugaba Buhari ya yada wasu hotunan shugaban da gwamnan ta shafin Twitter.

Asali: Legit.ng

Online view pixel