Raba kafa: Dan takarar shugaban kasa a PDP, Bala ya lallaba ya sayi fom din gwamna
- 'Yan siyasar kasar nan sun iya ba da mamaki, da alamu gwamnan Bauchi zai yi hakan a zaben 2023 mai zuwa
- Ana kyautata zaton gwamnan ya sayi fom din takara na gwamna a jiharsa duk da nuna sha'awar gaeje Buhari
- Sai dai, akwai batutuwa a kasa da har yanzu basu fito ba game da lamarin, wanda na kusa dashi suka musanta
Yayin da Bala Mohammed ke cikin jerin 'yan takarar shugaban kasa na PDP, a boye ya lallaba ya sayi fom din takarar komawa kujerar gwamnan jihar Bauchi a wa'adi na biyu, kamar yadda Premium Times ta ce ta samo.
Gwamna Mohammed dai zai cika wa'adinsa na farko a matsayin gwamnan jihar Bauchi ne a 2023, kuma zai iya sake neman takarar gwamnan a karo na biyu.
An sha hasashe kan wanda zai gaje shi a 2023 bayan da ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya a kwana nan.
Daya daga cikin irin wadannan hasashe ya nuna cewa sakataren gwamnatin jihar Ibrahim Kashim ya shiga wata yarjejeniya da gwamnan domin ya zama mai rike masa da mukaminsa.
A cewar hasashen, Kashim ya yi murabus ne a asirce kuma ya sayi fom din tsayawa takarar gwamna na jam’iyyar kuma za a dama dashi a zaben fidda gwani.
Idan ya yi nasara, Bala Mohammed bai yi nasara ba a yunkurinsa na neman tikitin takarar shugaban kasa na PDP, to zai koma gefe Bala Mohammed ya maye gurbinsa, in ji wasu batutuwan.
Sai dai masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da ke da masaniya kan abubuwan da ke faruwa a sakatariyar PDP ta jihar sun yi watsi da wannan hasashe da cewa ba gaskiya ba ne.
Ba wai ba, da gaske Bala Mohammed ya sayi fom din takara
Sun shaida wa wannan jaridar ta Premium Times cewa Bala Mohammed ba wai a asirce ya sayi fom din takarar gwamna a jihar ba har ma an tantance shi kuma ya cancanci a fafata dashi a lokacin zaben fidda gwani.
Wannan batu na Bala dai na iya zama tabbaci ga maganar Nyesom Wike, dan takarar shugaban kasa na PDP da ya zargi wasu gwamnoni da sayen fom din takarar gwamna bayan nuna sha'awar takarar shugabancin kasa a PDP.
A watan da ya gabata ne dai aka yanke shawarar zaban Bala Mohammed da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, a matsayin ‘yan takarar daga yankin Arewa a lokacin zaben fidda gwani na jam’iyyar.
A bangare guda, an samu cikas yayin da sauran 'yan takara daga yankin suka yi watsi da wannan shawarar.
A dawo kan batun sayen fom na gwmana Bala Mohammed, wasu na kusa da shi sun musanta batun, kana sun ki yin karin haske game da halin da ake ciki.
Gwarzon Dimokradiyya: Za a karrama shugaba Buhari da babbar lambar yabo
A wani labarin kuma, nan ba da jimawa ba za a karrama shugaban kasa Muhammadu Buhari da lambar yabo ta gwarzon dimokuradiyya, wanda majalisar ba da shawara ta jam’iyyu (IPAC) za ta ba shi.
Jaridar PM News ta ruwaito cewa, Engr. Yusuf Yabagi, shugaban jam'iyyar ADP kuma kodinetan IPAC ne ya sanar da hakan a ranar Talata 26 ga watan Afrilu yayin wata liyafar buda baki da Buhari a Abuja.
Yabagi ya ce za a karrama Buhari ne saboda sanya hannu a kan dokar zabe mai dumbun tarihi domin tana wakiltar sauyi da zai tabbatar da zaman lafiya da karbuwa da zabuka a kasar.
Asali: Legit.ng