Shehu Sani Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Har Yanzu Najeriya Ta Kasa Magance Matsalar Tsaro

Shehu Sani Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Har Yanzu Najeriya Ta Kasa Magance Matsalar Tsaro

  • Sanata Shehu Sani ya ce an kasa kawo karshen rashin tsaro a Najeriya ne saboda ko dai shugaban kasa ya cika kunya ko kuma ba ya da jajircewar daukar mataki akan na kasa da shi
  • A ranar Asabar tsohon sanatan ya bayyana hakan yayin tattaunawa akan rashin tsaro da kuma zaben 2023 mai karatowa inda ya ce dole sai an tsaya tsayin-daka sannan a samu mafita
  • A cewarsa idan kana jagorantar jami’an tsaro, karamar hukuma ko jiha kuma matsaloli su na ta aukuwa a yankinka, aikin shugaban kasa ne tumbukeka daga madafun iko

Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya ce saboda rashin jajircewar shugaban kasa ko kuma kunyarsa ta yi yawa akan na kasa da shi ne ya sa ya kasa kawo karshen rashin tsaro, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shehu Sani: Tuni Da Buhari Ya Shirya Zanga-Zanga Idan Da Jonathan Ne Ya Tara Bashi Kamar Yadda Ya Yi

Sani ya yi wannan maganar ne a ranar Asabar yayin da Daily Trust ta Twitter ta gayyace shi a matsayin bako mai jawabi inda ya yi magana akan rashin tsaro da kuma zaben 2023.

Rashin Shugaban Kasa Jajirtacce Yasa Rashin Tsaro Ke Karuwa a Najeriya, Shehu Sani
Rashin tsaro yana karuwa ne saboda ba mu da jajirtaccen shugaban kasa, Shehu Sani. Hoto: Daily Trust.
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce na kasa da Buhari ma sungaza, ya kamata sauya su ya dora wasu

Kamar yadda ya ce:

“Mutanen da ke kan madafun iko su na ta gazawa kuma za su ci gaba da gazawa saboda shugaban kasar mu ba ya da karfin daukar mataki akan na kasa da shi.
“Idan ka jagoranci jami’an tsaro, sojoji, ko kuma karamar hukuma ko jiha, kuma ana ci gaba da kai hare-hare yankinka, to babu amfani ka kuma aikin shugaban kasa ne korar irin wannan, ya maye gurbinsa da wani daban.
“Wani lokaci matsalolin tsaro su na bukatar irin haka. Akwai zargin cewa har da jami’an tsaro ake hada kai ana rura wutar rashin tsaro.”

Kara karanta wannan

Kuri'u miliyan 11 ke jirana: Atiku ya bayyana yadda 'yan Najeriya ke kaunarsa

Ya koka akan kara wa’adin shugabannin tsaro da gwamnati ta yi

Daily Trust ta nuna inda Sani ya kara da cewa ba a taba daukar wani tsatstsauran mataki ba a Najeriya akan wadanda suka gaza, hakan ya sa ya bukaci shugaban kasa ya yi aikinsa yadda ya dace.

Ya ci gaba da cewa bai dace mutum ya zura ido yana ganin wanda ya dauka aiki yana zaune ba ya tabuka abin kirki ba.

Ya koka akan yadda gwamnati ta kara wa Shugaban Hukumar Gidajen Gyaran Halin Najeriya, shugabannin tsaro da sauransu wa’adi.

A cewarsa babu wata nasarar da aka samu bayan aiwatar da hakan kuma ya kamata shugaban kasa ya kara dagewa wurin yin aikinsa.

Ba a Taɓa Gwamnatin Da Ta Kai Ta Buhari Rashawa Ba: Naja'atu Ta Ragargaji Buhari Kan Yafewa Dariya Da Nyame

A wani rahoton, Naja’atu Mohammed, mamba a Hukumar Dauka da Ladabtar ‘Yan sanda, PSC, ta caccaki Shugaban Kasa Muhammadu Buhari akan yafe wa tsofaffin gwamnoni, Joshua Dariye na Jihar Filato da Jolly Nyame na Jihar Taraba.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Da Ke Son Gadon Kujerar Buhari Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ƴan Ta'adda Suka Adabi Najeriya

Daily Nigerian ta ruwaito yadda a ranar Alhamis, majalisar jiha, wacce Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta ta yafe wa Dariye da Nyame tare da wasu fursinoni 157 da ke fadin kasar nan.

An yanke wa Dariye, wanda ya rike kujerar gwamnan Jihar Filato tsakanin 1999 da 2007, shekaru 14 a gidan yari saboda satar N1.16b, sannan an yanke wa Nyame shekaru 12 a gidan yari akan satar N1.6b, wanda ya yi gwamnan Jihar Taraba tsakanin 1999 da 2007 a shekarar 2020.

Asali: Legit.ng

Online view pixel