Shehu Sani: Tuni Da Buhari Ya Shirya Zanga-Zanga Idan da Jonathan Ne Ya Tara Bashi Kamar Yadda Ya Yi

Shehu Sani: Tuni Da Buhari Ya Shirya Zanga-Zanga Idan da Jonathan Ne Ya Tara Bashi Kamar Yadda Ya Yi

  • Sanata Shehu Sani ya ce da yanzu Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya shirya zanga-zanga idan da gwamnatin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ce ta tara bashi kamar ta sa
  • Sanatan wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar tarayya ta 8, ya ce gwamnatin Buhari ba ta yi kokari ba musamman dangane da basukan da ta tara mai yawa
  • A cewarsa Buhari bai yi komai ba a ofishinsa inda ya ce duk nasarorin da mulkinsa ya yi ba komai ba ne in har bai samar da tsaro a Najeriya ba

Sanata Shehu Sani ya ce idan da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ne ya tara bashi kamar yadda gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi, da tuni ya shirya zanga-zanga, Daily Trust ta ruwaito.

A wata tattaunawa da Daily Trust ta yi da jama’a a Twitter, Sanatan wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisa ta 8, ya bayyana rashin kokarin gwamnatin.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Da Ke Son Gadon Kujerar Buhari Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ƴan Ta'adda Suka Adabi Najeriya

Shehu Sani: Tuni Da Buhari Ya Shirya Zanga-Zanga Idan da Jonathan Ne Ya Tara Bashi Kamar Yadda Ya Yi
Tuni Da Buhari Ya Shirya Zanga-Zanga Idan da Jonathan Ne Ya Tara Bashi Kamar Yadda Ya Yi, In Ji Shehu Sani. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Kamar yadda ya ce:

“Najeriya ba ta taba fuskantar lokacin da ta tara bashi mai tarin yawa kamar wannan lokacin ba. Ko ta ina sai rancen kudade ake yi.”

Ya ce duk wata nasarar da Buhari ya ke tunanin ya samu ta tashi a tutur babu in har bai ba ‘yan Najeriya tsaro ba.

Sani, wanda ya zargi Buhari da rashin jajircewa a ofishinsa, ya ce ya yi mamakin dalilin da ya hana shi sabunta ministocinsa.

Buhari ya taba jagorantar zanga-zanga a 2014

A lokacin da Buhari ya na takarar shugaban kasa karkashin inuwar jam’iyyar APC, ya jagoranci dubbannin jama’a wurin yin zanga-zanga a Abuja.

Masu zanga-zangar sun zargi gwamnatin PDP da mayar da Boko Haram siyasa.

Sun kuma zargi Goodluck Jonathan da PDP da rashin jajircewa da dagewa wurin kawo gyara a kasar nan.

Kara karanta wannan

Abubuwan da shugaba Buhari ya faɗa mun har na ayyana shiga takarar shugaban ƙasa, Gwamnan APC

Sun kira zanga-zangar da ‘Gangamin Ceto’, wacce su ka shirya don janyo hankalin duniya akan yadda a cewarsu jam’iyyar da su ke adawa da ita ta dabaibaye ‘yan sandan Najeriya da sauran jami’an tsaro.

Ba a Taɓa Gwamnatin Da Ta Kai Ta Buhari Rashawa Ba: Naja'atu Ta Ragargaji Buhari Kan Yafewa Dariya Da Nyame

A wani rahoton, Naja’atu Mohammed, mamba a Hukumar Dauka da Ladabtar ‘Yan sanda, PSC, ta caccaki Shugaban Kasa Muhammadu Buhari akan yafe wa tsofaffin gwamnoni, Joshua Dariye na Jihar Filato da Jolly Nyame na Jihar Taraba.

Daily Nigerian ta ruwaito yadda a ranar Alhamis, majalisar jiha, wacce Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta ta yafe wa Dariye da Nyame tare da wasu fursinoni 157 da ke fadin kasar nan.

An yanke wa Dariye, wanda ya rike kujerar gwamnan Jihar Filato tsakanin 1999 da 2007, shekaru 14 a gidan yari saboda satar N1.16b, sannan an yanke wa Nyame shekaru 12 a gidan yari akan satar N1.6b, wanda ya yi gwamnan Jihar Taraba tsakanin 1999 da 2007 a shekarar 2020.

Kara karanta wannan

Ba don jajircewar Buhari ba da rashin tsaron Najeriya ya fi haka muni, Gwamnan dake son takara

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164