Ma'aikatan banki 2 sun shiga hannun EFCC kan laifin sace miliyoyin kudi na kwastoman da ya mutu

Ma'aikatan banki 2 sun shiga hannun EFCC kan laifin sace miliyoyin kudi na kwastoman da ya mutu

  • Babbar kotun jihar Cross River ta garkame wasu ma'aikatan banki biyu kan laifin satan kudi daga asusu bankin wani kwastoma da ya mutu a jihar.
  • Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC ce ta gurfanar da su.
  • A cewar lauyan EFCC, an gurfanar da su kan laifin damfara, yaudara da amfani da takardun bogi

Birnin Calabar - Ma'aikatan bakin biyu masu suna - Titus Chima Nwankwo da Utibe-Abasi Ifiok George - sun saci kudi N2,900,000 daga asusun kwastoman da ya mutu.

An fara gurfanar da su ne ranar 16 ga Yuni, 2021 lokacin da aka shigar da kararsu cewa sun kirkiri sanya hannun wani Godfried Francis Ossi, wanda ya mutu.

A cewar jawabin da EFCC ta fitar, matasan biyu a ranar Talata, 26 ga Afrilu sun amsa laifinsu.

Kara karanta wannan

Sabon Harin Filato: Yan bindiga sun kashe 5, sun yi garkuwa da mutum 20

Ma'aikatan banki 2
Ma'aikatan banki 2 sun shiga hannun EFCC kan laifin sace miliyoyin kudi na kwastoman da ya mutu Hoto: EFCC
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sakamakon haka, lauyan EFCC, Joshua Abolarin, ya bukaci kotu ta yanke musu hukunci kuma ta jefasu kurkuku..

Shi kuwa Alkalalin, Elias Abua, ya jefa Utibe-Aashi zaman gidan gyara halin watanni uku ko ya biya tarar N100,0000.

Shi kuwa Titus Chima, kotun ya jefashi kurkukun watanni 3 ko ya biya tarar N50,000.

Yan bindiga sun kai wa motar kudi farmaki a Imo

A Imo kuwa, 'Yan bindiga sun bude wuta kan wata motar banki dake tafiya daga Mbaise zuwa Owerri a ranar Alhamis a karamar hukumar Mbaise.

Vanguard ta tattaro cewa, lamarin ya faru wurin karfe 2 na rana a Ogbor Nguru dake Nwankwo a karamar hukumar Mbaise a jihar.

The Cable ta ruwaito cewa, an gano cewa, 'yan bindigan na kyautata tsammanin cewa motar dankare take da kudi kuma za ta kai su inda ya dace ne amma sai suka same ta babu komai ciki.

Kara karanta wannan

Sau Ɗaya DSS Ke Bawa Nnamdi Kanu Abinci a Kowanne Rana, In Ji Lauyan IPOB

Wani ganau ba jiyau ba ya sanar da yadda 'yan bindigan suka dinga harbi babu kakkautawa inda direban motar da wasu mutum biyu a kokarinsu na tserewa suka dinga tintsirawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel