Sabon Harin Filato: Yan bindiga sun kashe 5, sun yi garkuwa da mutum 20

Sabon Harin Filato: Yan bindiga sun kashe 5, sun yi garkuwa da mutum 20

  • Tsagerun yan bindiga sun kai farmaki hanyar Sabon Gari-Kampani da ke karamar hukumar Wase ta jihar Filato
  • A yayin harin, sun kashe mutane biyar ciki harda wani dan sa kai, sun kuma yi garkuwa da wasu mutum 20
  • Lamarin ya faku ne a lokacin da mutane da abun ya ritsa da su ke a hanyarsu ta dawowa daga kasuwa

Filato - Akalla fasinjoji biyar ciki harda wani dan sa kai aka kashe a hanyar Sabon Gari-Kampani da ke karamar hukumar Wase ta jihar Filato.

Daily Trust ta rahoto cewa yan bindiga da suka addabi yankin ne suka kashe mutanen.

Sabon Harin Filato: Yan bindiga sun kashe 5, sun yi garkuwa da mutum 20
Sabon Harin Filato: Yan bindiga sun kashe 5, sun yi garkuwa da mutum 20 Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

A cewar Abdullahi Usman, wani mazaunin garin Wase, an yiwa dan bangar da wani mutum kautan bauna ne, yayin da aka kashe sauran mutane ukun a yayin da yan bindigar ke tsayar da motoci suna bincikarsu.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja

Usman ya kara da cewar an yi awon gaba da fasinjoji fiye da guda 20 a harin.

Ya ce:

“Dan bangar da wani mutum na a kan babur daga Sabon- Gari zuwa Kampani lokacin da yan bindigar suka far masu. Sun kashe su sannan suka yi awon gaba da babur din.
"Daga bisani, lokacin da mazauna kauyen ke hanyarsu ta dawowa bayan kasuwa, sai aka far masu sannan aka yi awon gaba da su. An kashe uku daga cikinsu."

Da aka tuntube shi domin jin ta bakinsa, kakakin Operation Safe Haven, Major Ishaku Takwa, ya ce ba a sanar masa da faruwar lamarin ba, amma ya yi alkawarin kira daga baya.

Hada SIM/NIN: An bayyana babban matsalar 'yan ta'adda a arewa maso gabas

Kara karanta wannan

Sokoto: Bishop Kukah ya yi martani kan kashe dalibar da ta yi batanci ga Annabi

A wani labari na daban, hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC) ta bayyana a ranar Juma’a, 29 ga watan Afrilu, cewa hada lambobin NIN da layukan SIM na haifar da sakamakon da ake bukata domin a yanzu yan ta’adda da yan fashi na fuskantar matsala wajen aiwatar da ayyukansu.

Hukumar ta yi bayanin cewa aiwatar da wannan manufa da aka yi, ya hana yan ta’adda da yan bindiga samu damar yin amfani da hanyoyin sadarwa, jaridar The Nation ta rahoto.

Hukumar ta bayar da tabbacin cewa:

“Abun da suke yi a yanzu shine amfani da wayoyin wadanda suka sace don yin magana yayin da suke ajiye mutanen wurare masu nisa. Amma zuwa dan lokaci, wannan dabaru nasu ba zai tsiratar da su ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel