Sau Ɗaya DSS Ke Bawa Nnamdi Kanu Abinci a Kowanne Rana, In Ji Lauyan IPOB

Sau Ɗaya DSS Ke Bawa Nnamdi Kanu Abinci a Kowanne Rana, In Ji Lauyan IPOB

  • Ifeanyi Ejiofor, lauyan shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu ya koka kan wasu matsaloli da ya ce wanda ya ke karewa ke fuskanta
  • Ejiofor ya ce yayin ziyarar da ya kai wa Kanu a ranar Alhamis da ta gabata a hedkwatar DSS, ya fada masa da kyar ya ke samun abinci sau daya a rana
  • Hakazalika, lauyan ya sake kokawa kan rashin amincewa Kanu ya canja kayan jikinsa duk da cewa kotu ta umurci DSS ba bari ya canja kayan

Lauyan Kungiyar Masu Neman Kasar Biafra, IPOB, Ifeanyi Ejiofor, ya yi ikirarin cewa ba a bari Nnamdi Kanu, shugaban IPOB da ke hannun DSS ya ci abinci fiye da sau daya a kowanne rana, rahoton Vanguard.

Ejiofor, ya bayyana wa manema labarai hakan ne a ranar Juma'a a Owerri bayan ya ziyarci Kanu a ofishin DSS inda ake tsare da shi a Abuja, ranar Alhamis da ta gabata kamar yadda Africa Prime News ta rahoto.

Kara karanta wannan

An sake samun wani babban Gwamna a APC da yake tunanin fitowa Shugaban kasa

Sau Ɗaya DSS Ke Bawa Nnamdi Kanu Abinci a Kowanne Rana, In Ji Lauyan IPOB
Sau Ɗaya DSS Ke Bawa Nnamdi Kanu Abinci a Kowanne Rana, Lauyan IPOB. Hoto: Vanguard.
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce wannan na cikin korafin da Kanu ya masa yayin ganawarsu. Ejiofor ya kara da cewa halin da Kanu ke ciki na kara tabarbarewa domin DSS ta hana shi canja kaya duk da kotu ta nanata a bashi damar yin hakan.

Lauyan Kanu ya koka kan yadda DSS ke hana wanda ya ke karewa samun isashen abinci da canja tufafi

A cewar lauyan na IPOB:

"Bisa umurnin kotu, sun ziyarci wanda muke karewa Onyendu Mazi Nnamdi Kanu a hedkwatar DSS yau. Mun tattauna batutuwa na sharia masu muhimmanci.
"Cigaba da saka kaya daya da Onyendu ke yi abin damuwa ne saboda DSS sun ki yarda ya canja kayan duk da umurnin kotu.
"Abin takaici shine har zuwa yau da muka ziyarce shi, ba a bawa Onyendu kaya ya canja na jikinsu ba."

Kara karanta wannan

Tashin Bama-Bamai: Ya Zama Dole Ƴan Najeriya Su Fara Kare Kansu, In Ji Ƙwararru a Ɓangaren Tsaro

Ya cigaba da cewa:

"Onyendu ya kuma sanar da mu cewa an dena bashi abinci yadda ya kamata. Da wuya Onyendu ke samun abinci sau daya a rana, hakan na sa lafiyarsa na tabarbarewa."

Ejiofor ya ce har yanz DSS sun ki biyayya ga umurnin kotu duk da cewa kowa ya sani babu wanda ya fi karfin doka a ko ina a duniya.

Ya ce za su cigaba da iya kokarinsu har sai sun tabbatar da cewa an magance matsalolin da Kanu ke fuskanta.

Kaduna: Lauya Ya Yi Ƙarar Wani Mutum a Kotun Shari'a Saboda Ƙin Biyansa N100,000 Kuɗin Aikinsa

A wani rahoton, Wata kamfanin lauyoyi a Kaduna mai suna Moonlight Attorneys, a ranar Litinin, ta yi karar wani Yusha'u Abdullahi a kotun shari'a saboda kin biyan kudin N100,000 kudin aikin da suka masa.

Lauyan wanda ya shigar da karar, Atiku Abdulra'uf, ya bayyana cewa wanda aka yi karar ya nemi wanda ya shigar da karar ya yi masa aiki, kuma suka amince zai biya adadin a matsayin kudin aiki, rahoton Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

Abin Da Maƙarfi, Fayose, Da Wasu Shugbannin PDP Suka Ce Game Da Ƙishin-Ƙishin Ɗin Komawar Jonathan Zuwa Jam'iyyar APC

Ya yi bayanin cewa bayan an kammala aikin, wanda aka yi karar ya ki biyan kudin duk da yarjejeniya da suka yi, hakan yasa wanda ya shigar da karar ya taho kotu don a bi masa hakkinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel