Sojoji sun tartwatsa gidan wani babban matsafi dake taimakon ýan ta’adda a jihar Benuwe

Sojoji sun tartwatsa gidan wani babban matsafi dake taimakon ýan ta’adda a jihar Benuwe

Rundunar Sojojin Najeriya ta musamman ta 707 ta kai farmaki gidan wani kasurgumin boka, Tordue Gber wanda aka fi sani da suna Tiv Swem, inda suka kasha shi a ranar Litinin 29 ga watan Janairu.

Kaakakin rundunar Sojin Najeriya, Birgediya SK Usman ne ya bayyana haka cikin wata sanarwar da ya fitar, inda yace Tiv Swem ne bokan dake daure ma yan ta’addan kabilar Tiv dake kai hare hare a jihar ta Benuwe.

KU KARANTA: Sojojin kamaru guda 80 sun kai hare hare a sansanonin yan gudun hijira a Najeriya

Sojojin sun kai masa harin ne a gidansa dake kauyen Tor-Dunga, cikin garin Katsina Ala, inda suka samu nasarar cafke duk wadanda suke cikin gidan a wannan lokaci, kamar yadda SK Usman ya bayyana.

Sojoji sun tartwatsa gidan wani babban matsafi dake taimakon ýan ta’adda a jihar Benuwe
Gawar matsafin da abokinsa

Majiyar Legit.ng ta ruwaito run da dadewa jami’an tsaro suke neman matsafin tare da wani mai suna Gana wurjanjan, musamman tun bayan da aka gani shi ne ke baiwa Gana tsafe tsafen da yake amfani da su wajen tsere ma jami’an tsaro idan ya aikata ta’asa.

Haka zalika a gidansa ne yan fashi da yan ta’addan dake garuruwan Taraba, Nassarawa da Benuwe ke haduwa tare da shirya yadda zasu kai hare hare da kuma zabar inda zasu kai harin.

Sojoji sun tartwatsa gidan wani babban matsafi dake taimakon ýan ta’adda a jihar Benuwe
Gidan

Don ko a ranar an kama shi ne tare da wani abokinsa Atoo Kuwe Francis a lokacin da suke shirya yadda zasu kai ma wani mutumi hari mai suna, Zaya tare da sace shi a kauyen Tse Bente, daga cikin abubuwan da aka gani a gidan suna hada da kirar Bindigu daban daban, Babura, alburusai da kayan tsafe tsafe.

Sojoji sun tartwatsa gidan wani babban matsafi dake taimakon ýan ta’adda a jihar Benuwe
Gidan

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng