Hada SIM/NIN: An bayyana babban matsalar 'yan ta'adda a arewa maso gabas

Hada SIM/NIN: An bayyana babban matsalar 'yan ta'adda a arewa maso gabas

  • Hukumar sadarwa ta Najeriya ta bayyana babban kalubalen da yan fashi da yan ta’adda ke fuskanta
  • A cewar hukumar, yan bindiga na fuskantar matsala da ayyukansu a yan baya-bayan nan sakamakon hada NIN da layukan SIM
  • NCC ta yi bayanin cewa wannan tsarin ya shafi hanyar sadarwar yan bindiga da yan ta’adda a kasar

Hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC) ta bayyana a ranar Juma’a, 29 ga watan Afrilu, cewa hada lambobin NIN da layukan SIM na haifar da sakamakon da ake bukata domin a yanzu yan ta’adda da yan fashi na fuskantar matsala wajen aiwatar da ayyukansu.

Hukumar ta yi bayanin cewa aiwatar da wannan manufa da aka yi, ya hana yan ta’adda da yan bindiga samu damar yin amfani da hanyoyin sadarwa, jaridar The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan Shi'a da jamian tsaro sun yi arangama, soji sun harbi mutum 8 a Zaria

Hada SIM/NIN: An bayyana babban matsalar 'yan ta'adda a arewa maso gabas
Hada SIM/NIN: An bayyana babban matsalar 'yan ta'adda a arewa maso gabas Hoto: Nigerian Communications Commission
Asali: Facebook

Hukumar ta bayar da tabbacin cewa:

“Abun da suke yi a yanzu shine amfani da wayoyin wadanda suka sace don yin magana yayin da suke ajiye mutanen wurare masu nisa. Amma zuwa dan lokaci, wannan dabaru nasu ba zai tsiratar da su ba."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daraktan sa ido da tabbatar da bin doka da oda na NCC, Mista Ephraim Nwokonanya ne ya bayyana hakan a hedkwatar hukumar da ke Abuja a lokacin da yake jawabi ga manema labarai da suka halarci taron karawa juna sani na kwana daya da hukumar ta shirya.

Ya samu wakilcin shugaban sashen bin doka da oda da tabbatar da doka, Mista Alkasim Umar , rahoton Vanguard.

Ya ce an samu ci gaba mai kyau dangane da hada NIN da SlM domin magance matsalolin ta’addanci da sace-sacen mutane da kuma fashi da makami a kasar.

Kara karanta wannan

Katsina: 'Yan sanda sun dakile harin 'yan bindiga, sun ceto wasu mata, sun kwato AK47

Matakai masu sauki da zaka bi wajen hada layin wayarka da NIN yayinda gwamnati ta toshe layukan 72m

A gefe guda, mun kawo a baya cewa bayan wata da watanni tana dage wa'adin rufe layukan wadanda basu hada lambar katin zaman dan kasa NIN da layukan waya ba, gwamnatin tarayya a ranar Litinin, 14 ga Afrilu, ta umurci kamfanin sadarwa su hana kira fita daga duk wani layin da ba'a hada ba.

Sakamakon wannan umurni, an toshe layuka milyan 72.77 daga kiran waya sai sun hada layukansu.

Legit ta tattaro muku yadda zaku iya hada layukan wayarku da NIN ga masu amfani da MTN, Glo, Airtel, and 9mobile.

Asali: Legit.ng

Online view pixel