Hotuna: Sojin Najeriya sun ragargaji Boko Haram, sun halaka Amir da shugaban malaman 'yan ta'addan

Hotuna: Sojin Najeriya sun ragargaji Boko Haram, sun halaka Amir da shugaban malaman 'yan ta'addan

  • Dakarun sojin Najeriya sun yi nasarar halaka Amir da shugaban malaman 'yan ta'addan Boko Haram a Borno
  • A wallafar rundunar a shafinta na Twitter, ta bayyana cewa dakarunta sun kai samamen yankin Manjo Ali Qere inda suka ragargaji 'yan ta'adda
  • Cike da nasara sojojin suka samu kwace miyagun makamai da suka hada da bindigogi da kuma harsasai masu yawa

Borno - Labari mai dadi da ke zuwa daga rundunar sojin Najeriya shi ne na nasarar da suka samu a samamen da suka kai karkashin Operation Desert Sanity.

Zakakuran sojojin Najeriyan sun samu nasarar halaka mayakan ta'addanci na Boko Haram da ISWAP da ke yankin Manjo Ali Qere a jihar Borno.

Hotuna: Sojin Najeriya sun ragargaji Boko Haram, sun halaka Amir da shugaban malaman 'yan ta'addan
Hotuna: Sojin Najeriya sun ragargaji Boko Haram, sun halaka Amir da shugaban malaman 'yan ta'addan. Hoto daga @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, 28 ga watan Afirilun 2022 inda sojojin suka sheke Amir da wani shugaban malaman 'yan ta'addan na Galta a samamen.

Kara karanta wannan

An damke sojan da ke hada kai da ISWAP, ya bindige kansa ana shirin mika shi bariki

A hotunan da rundunar ta wallafa a shafinta na Twitter, an ga makamai da suka hada da bindigogi da harsasai wadanda sojojin suka yi nasarar kwacewa daga hannun 'yan ta'addan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An damke sojan da ke hada kai da ISWAP, ya bindige kansa ana shirin mika shi bariki

A wani labari na daban, hukumomi sun damke wani soja da ke hada kai da mayakan ta'addanci na ISWAP wurin kai farmaki amma ya bindige kansa yayin da ake kokarin mika shi bariki.

PRNigeria ta tattaro cewa, sojan yana daya daga cikin sojojin bataliyoyin rundunar sojan Najeriya da ke yaki da rashin tsaro a arewa maso gabas kuma jami'an binciken sirri na sojoji ne suka gano hannunsa a farmakin kwanakin nan da aka kai gidajen karuwai da na giya da ke Geidam da Gashua a jihar Yobe.

Kara karanta wannan

Hotuna: Yadda sojojin Najeriya suka ragargaji 'yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno

"Yana da hannu cikin farmakin kwanakin nan na Geidam da Gashua a jihar Yobe. An kama shi yayin da yake yunkurin tserewa bayan ya gane cewa jami'an binciken sirri suna bibiyar lamurransa da 'yan ta'addan.
“Bayan an saka masa ankwa, cike da kwarewa ya kwace bindiga daga hannun daya daga cikin wadanda ke tsare da shi kuma ya kashe kansa."

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel