Yan bindigan sun yi awon gaba da wani Basarake a Kaduna, sun bukaci abu 2 fansa

Yan bindigan sun yi awon gaba da wani Basarake a Kaduna, sun bukaci abu 2 fansa

  • Miyagun yan bindiga sun yi awon gaba da Magajin Garin Rijana tare da wasu manoma a jihar Kaduna
  • Mazauna ƙauyen sun bayyana cewa maharan sun tuntuɓi shuwagabannin al'umma, sun lissafo abubunwan da suke so a matsayin fansa
  • Rijana sanannen kauye ne kasancewarsa a kan babbar hanyar Kaduna-Abuja, wacce yan bindiga suka addaba

Kaduna - Yan bindiga sun yi garkuwa da Ayuba Dodo Dakolo, dagacin kauyen Rijana, ƙaramar hukumar Kachia a jihar Kaduna.

Daily Trust ta tattaro cewa sun sace Dagacin ne tare da wasu manoma a Kurmi, kusa da Chikwale dake yankin na Kachia.

Kauyen Rijana na kan babbar hanyar Kaduna-Abuja da mutane ke yawan bi, kuma hanyar ta yi ƙaurin suna saboda yawan harin yan bindiga, waɗan da ke tare matafiya su sace mutane.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan bindiga sun kashe shugaban jam'iyyar APC a yankin Kaduna

Yan bindiga sun kai hari Kaduna.
Yan bindigan sun yi awon gaba da wani Basarake a Kaduna, sun bukaci abu 2 fansa Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Wata majiya daga kauyen, ta shaida wa manema labarai ranar Alhamis cewa, yan bindigan sun tuntuɓi shugabannin ƙauyen, sun zayyana musu abu biyu da suke bukata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoto ya nuna cewa wasu daga cikin abubuwan da suka zayyano suƙa buƙata ya haɗa da Galan ɗin Man Fetur, Baƙin man inji, da Sigari.

Wani mazaunin ƙauyen ya ce:

"Mun yi magana da shugaban mu kuma yana cikin koshin lafiya, a yanzun sun nemi mu kai musu katin waya kuma sun yi barazanar kashe shi idan muƙa ki aiwatarwa."

Shin yan sanda sun san halin da ake ciki?

Yayin da aka tuntubi kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, bai ɗaga kiran wayar ba bare jin ta bakin hukumar su kan sace Dagacin.

Amma wani babban jami'i ya shaida wa manema labarai cewa jami'an tsaro sun samu masaniya kan abun da ya faru.

Kara karanta wannan

Ana Shirin Sallah: Yan bindiga sun kashe Kwamandan jami'an tsaro, sun tarwatsa mutanen gari a Zamfara

A wani labarin na daban kuma Gwamna Wike ya ayyana neman ɗan majalisa ruwa a jallo kan abu ɗaya

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike , ya umarci a kama ɗan majalisar tarayya, Farah Dagogo ko ina ya shiga.

Wike ya dauki wannan matakin ne bisa zargin ɗan majalisar ya tura yan daba Sakariyar PDP dake Patakwal su ta da yamutsi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel