Limamin Aso Rock Ya Ankarar Da Buhari Kan Wasu Abubuwa Da Ka Iya Faruwa Gabanin Zaɓen 2023

Limamin Aso Rock Ya Ankarar Da Buhari Kan Wasu Abubuwa Da Ka Iya Faruwa Gabanin Zaɓen 2023

  • Babban limamin masallacin fadar shugaban kasa ya tunatar da Shugaba Buhari kan abubuwa da za su iya faruwa gabanin zaben 2023
  • Sheikh Abdulwahid Sulaiman, yayin wa'azinsa na rufe tafsirin watan Ramadana na bana ya shawarci Buhari ya tabbatar sadaukarwar da al'umma suka yi bai zama asara ba
  • Limamin ya kuma yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari, yana mai cewa shugaban kasar ya amfana da darrusan da watan na Ramadana ke koyarwa

Abuja - Babban limamin gidan gwamnati, Sheikh Abdulwahid Sulaiman, a jiya ya bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya cigaba da jajircewa ya cigaba da sanya kasa a gaba ya tabbatar cewa ba a yi asarar sadaukarwar da aka yi shekarun baya ba a yayin da zabe ke zuwa.

Limanin, a cewar sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasa, Garbe Shehu, ya fitar ya yi magana ne a Masallacin Gidan Gwamnati yayin rufe tafsir na bana da Buhari da wasu mutane suka halarta, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Da Ke Son Gadon Kujerar Buhari Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ƴan Ta'adda Suka Adabi Najeriya

Limamin Aso Rock Ya Ankarar Da Buhari Kan Wasu Abubuwa Da Ka Iya Faruwa Gabanin Zaɓen 2023
Kada ka bari a yi asarar sadaukarwar da aka yi a baya, Limanin Aso Rock ya shawarci Buhari. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Sheikh Sulaiman ya ce Shugaba Buhari ya amfana da darrusan da ke cikin watan Ramadan

Shehu ya ce limamin, Sheikh Sulaiman ya jinjinawa Buhari saboda sadaukarwarsa da gaskiya da rikon amana da aikin da ya yi wa kasa, rahoton Pulse Ng.

Ya ce Buhari ya amfana da darrusan da ke cikin watan na Ramadan a yayin da musulmi a kasashen duniya ke shirin bankwana da watan.

Shehu ya ce Shugaban Kasar ya hallarci tafsirin da aka yi a cikin watan Ramadana kuma ya rika gayyatar baki daban-daban zuwa fadarsa domin bude-baki (iftar).

Ya ce Buhari ya yi amfani da watan wurin amfana da darrusan da ke cikin watan Ramadan da suka hada da sadaukar da kai, kula da kyautatawa marasa galihu, habbaka hadin kan kasa da tallafawa sojoji a yayin da suke yaki don kawo karshen ta'addanci da wasu laifuka a kasar.

Kara karanta wannan

Bayan makonni biyu, har yanzu ba'ayi rabon ton 40,000 na hatsi da Buhari yace ayi ba

2023: Ƙungiyar musulmai ta buƙaci Gwamna Ugwuanyi ya fito ya nemi kujerar Buhari

A wani rahoton, kungiyar hadin kan al’ummar musulmi, UMUL ta bukaci dan kabilar Ibo ya tsaya takarar shugaban kasa idan 2023 ta zo, The Sun ta ruwaito.

Kungiyar ta musulmai ta ce lokaci ya yi da cikin yankuna biyar da ke kasar nan, ko wanne yanki zai samu adalci da daidaito da juna, hakan yasa take goyon bayan Igbo ya amshi mulkin Najeriya.

Kamar yadda kungiyar ta shaida, dama akwai manyan yaruka uku a Najeriya, Hausa, Yoruba da Ibo, don haka in har ana son adalci, ya kamata a ba Ibo damar mulkar kasa don kwantar da tarzomar da ke tasowa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164