Bayan mako biyu, har yanzu ba'ayi rabon ton 40,000 na hatsi da Buhari yace ayi ba

Bayan mako biyu, har yanzu ba'ayi rabon ton 40,000 na hatsi da Buhari yace ayi ba

  • Makonni biyu yanzu da umurnin Buhari, har yanzu ba'aji doriyar kayan hatsin da Buhari yace a raba ba
  • Buhari ya ce a fitar da buhuhunan hatsi don bikin Easter, Azumin wata Ramadana da karamar Sallah
  • Wasu majiyoyi sun bayyana dalilan da yasa har yanzu kayan hatsin basu bar Abuja ba duk da an ce a fara

Makonni biyu da suka gabata, Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurnin fitar da ton 40,000 na kayan hatsi daga runbun gwamnati don rabawa talakawan Najeriya albarkacin watar Ramadana, bikin Easter da Karamar Sallah.

Amma tun da aka kaddamar da rabon a birnin tarayya Abuja, har yanzu shiru ake ji ba'a ji doriyar wadannan kayan hatsi ba.

Ministan noma da raya karkara wanda ya kaddamar da rabon makonni biyun da suka gabata yace za'a raba ne don rage radadin hauhawar farashin kayan abinci a kasuwa a lokacin Azumi da Sallah.

Kara karanta wannan

Kada haka ta sake faruwa: Shugaba Buhari ya kadu da jin labarin salwantar rayuka 100 a Imo

Amma gashi azumi ya zo karshe, an gama hutun Easter, kuma gashi Sallah ta gabato amma babu labari.

Bayan mako biyu, har yanzu ba'ayi rabon ton 40,000 na hatsi da Buhari yace ayi ba
Bayan mako biyu, har yanzu ba'ayi rabon ton 40,000 na hatsi da Buhari yace ayi ba Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Abinda Ministan ya fada makonni 2 da suka gabata

A taron kaddamar da rabon kayan hatsin da sansanin yan gudun hijra dake Karmajiji, birnin tarayya Abuja, Ministan yace an fara rabon ne bisa umurnin Shugaban kasa.

Dr. Mohammad Mahmood Abubakar yace haka za'a raba kayan dukkan jihohin tarayya.

Yace:

"Gidaje da dama na bukatar taimakon abinci don rage wahalar yunwa da tsadar abinci da suke fama."

Diraktan sashen rumbun abinci, Sule Haruna, yace wannan ita ce manufar ajiyar abincin don rage radadi.

Me yasa ba'a fara rabon ba har yanzu

Daily Trust ta ruwaito cewa wasu majiyoyi a ma'aikatar noma sun ce akwai matsaloli da dama da suka hadasa jinkirin rabon kayan abincin, daga ciki akwai matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Yan bindiga sun sace wata mai taimakon talakawa da diyarta a Kaduna, sun nemi a biya N100m

Wata majiya tace:

"Ma'aikatar na gudun arangama da wadannan yaran (yan bindiga da yan ta'adda) da zasu kaiwa wadannan motocin abinci hari kuma su kashe mutane."

Wata majiyar daban tace har yanzu Minista ake sauraro ya saki kudin tafiyar da wadannan abinci.

Yadda za'a yi rabon

Ministan yayin hira da manema labaran fadar shugaban kasa bayan ganawa da shugaba Buhari ya ce cikin ton 40,000 da za'a saki, za'a baiwa ma'aikatar Hajiya Sadiya Farouq ton 12,000 don rabawa yan gudun hijra dake fadin tarayya.

An tattaro cewa kungiyar masu kiwon kaji ta Najeriya zasu samu ton 5000, yayinda gwamnatocin jihohi, kungiyoyin addini, dss zasu samu ton 23,0000.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags:
Online view pixel