Yan ta'adda na amfani da gidajen da muka bari suna bacci, yan gudun hijira
- Wasu mutanen da suka gudu suka bar kauyukan su saboda harin yan bindiga sun bayyana yadda yan ta'addan ke amfani da ɗakunan su
- A cewar mazauna wasu daga cikin ƙauyukan ƙaramar hukumar Munya da suka koma Minna, mahara na fito da kayan kwanciya su kwanta a kasan bishiyoyi
- Wani Muhammad Awwal ya ce yan uwan su da suka je shuka doya har yau ba su dawo ba
Niger - Mazauna kauyukan da yan bindiga suka fatattaka daga gidajen su a ƙaramar hukumar Munya ta jihar Neja sun faɗi wani sirrin wurin buyar yan ta'addan.
Mutanen sun bayyana cewa a halin yanzun yan ta'addan da suka addabi yankunan su, suna amfani da ɗakunan da suka bari wajen kwanciya da bacci.
Da yake zantawa da wakilin Daily Trust, ɗaya daga cikin mutanen da harin yan bindiga ya shafa wanda yake zaune a Minna yanzu, ya ce yan ta'addan suna fito da kyan kwanciyarsu don su sha iska a karkashin bishiyoyi da daddare.
Ya ce garuruwan Gunu da kuma Shakwata, waɗan da ba su wuce nisan Kilomita 20 ba daga Minna, yan ta'addan sun miada su tamkar na su.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Daga cikin wasu yankunan da lamari irin wannan ya shafa har da Kafana da Kurgbako duk dai a cikin ƙaramar hukumar Munya.
Rahoto ya nuna cewa wasu daga cikin mutanen da suka yi gudun hijira, wadan da suka bar Minna da nufin zuwa shuka Doya a kauyukan, an yi garkuwa da su.
Kauyukan da yan bindiga suka farmaka ranar Talata sun haɗa da, Kuchi, Kafana, Chibani da Wuloto, inda suka yi awon gaba da mutane mafi yawa maza.
Sun hana mu sana'ar mu ta noma - Awwal
Ɗaya daga cikin mutanen da suka baro gidajen su, Muhammad Awwal ya ce:
"Yan uwan mu sun koma shuka doya amma aka yi garkuwa da su, yan ta'addan sun shigo da ƙarfe 4:00 na yamma, dama zuwa muke a ranar mu dawo."
"Idan suka buɗe wurin ajiyar Doyar mu na gona suka ɗiba yadda ran su ke so, ba zasu rufe ba, hakan ke ba dabobi damar yi mana ɓarna."
Legit.ng Hausa ta zanta da wani ɗan yankin Shiroro, ɗaya ɗaga cikin kananan hukumomin da lamarin ya shafa, wanda ya tabbatar da munin abin da ke faruwa a wasu kauyukan Munya.
Mutumin, wanda ya nemi a ɓoye bayanansa, ya shaida wa wakilin mu cewa:
"Tabbas abinda ke faruwa a ƙauyukan Munya ya yi muna, ni ɗan Shiroro ne amma ina zuwa yankunan, akwai wani kauye mai suna Kuchi, a yankin Munya, yan ta'adda sun kori mutane sun zauna a wurin."
"Idan suka kawo hari nan Shiroro suka kwashi nutane can wajen ake zargin suna kai su, amma ba su shiga da su kauyen, a jeji suka aje su. Kullum sai sun kai hari, shiyasa mutane suka gudu."
A cewar mutumin mafi yawan mutanen da suka bar gidajen su, yanzun sun kom a yan gudun hijira a Minna, ko Gunu.
A wani labarin na daban kuma Gwamna Wike ya ayyana neman ɗan majalisa ruwa a jallo kan abu ɗaya
Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya umarci a kama ɗan majalisar tarayya, Farah Dagogo ko ina ya shiga
Wike ya dauki wannan matakin ne bisa zargin ɗan majalisar ya tura yan daba Sakariyar PDP dake Patakwal su ta da yamutsi.
Asali: Legit.ng