Magidanci ya cika bujensa da iska bayan matarsa ta haifa ƴan huɗu

Magidanci ya cika bujensa da iska bayan matarsa ta haifa ƴan huɗu

  • Cissé Abdullahi, ma tsar shagon siyar da taya ya nemi tserewa bayan matarsa ta haifa masa 'yan 4 ya nemi agaji daga gwamnatin jihar Legas da sauran masu hannu da shuni a fadin kasar
  • A cewarsa, N3,500 kacal gare shi a lokacin da aka sanar masa da cewa matarsa ta haifi 'yan hudun, wanda hakan ne yasa ya yi kokarin tserewa saboda ya rasa yadda zai yi
  • Ya cigaba da bayyana yadda asibiti ke binsu kudade, gashi basa da hanyar da zasu iya biya, duk da mahaifiyar 'ya'yan tayi godiya ga Ubangiji da kulawar da take samu a asibitin

Legas - Cissé Abdullahi, mai tsare shagon siyar da taya wanda ya yi yunkurin tserewa Jamhuriyar Benin bayan matarsa ta haifi 'yan hudu, ya roki gwamna Babajide Sanwo- Olu na Legas da sauran masu rajin tallafawa bil'adama da su taimaka masa wajen kula da jinjirayen.

Kara karanta wannan

Kada wanda ya kusanci matan Alaafin, an killacewa sabon sarki ne, 'Dan gargajiya

Abdullahi, mai shekaru 37, daga Ilorin, wanda ke zaune a Kumaoaji Phase 3, tashar motocin Baale a Oko-Afo cikin Olorunda LCDA, ya bayyanawa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) yadda yake da N3,500 kacal a aljihunsa a lokacin da ya samu labarin matarsa ta haifa masa 'yan hudu.

Magidanci ya cika bujensa da iska bayan matarsa ta haifa ƴan huɗu
Magidanci ya cika bujensa da iska bayan matarsa ta haifa ƴan huɗu. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC
"Ina kan hanyar dawowa daga Apapa inda nake saida tayoyi sanda labarin matata ta haifa min 'yan hudu ya riske ni a Babban asibitin Badagry.
"Abu ne mai kyau, amma ban taba sa ran 'yan hudu ba, saboda hoton da muka yi na karshe ya nuna cewa 'yan biyu ne.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A lokacin da na isa gida, na yanke shawarar ranta a na kare zuwa Jamhuriyar Benin, saboda bani da kudin kula da 'yan hudun.
"Amma da na isa iyakar Seme, ina kokarin tsallakawa nayi ido biyu da shakikin abokina wanda ya yi mamakin gani na a iyakar kasar misalin karfe 9:00 na dare."

Kara karanta wannan

Matar aure ta sha da kyar, saurayinta ya nemi halakata yayi tsafi da ita

Premium Times ta ruwaito cewa, ya kara da cewa:

"Hakan ya tilasta min bayyana masa dalilin da yasa naso ficewa daga kasar, daga karshe dai, ya lallashe ni da in koma ga iyalina, tare da yi min alkawarin zai tallafa min," a cewarsa.

Abdullahi ya cigaba da labarta yadda tun bayan dawowarsa gida ga matarsa da 'ya'yansa, wanda kadai yake tallafa masa shi ne wannan abokin nasa.

Sabon mahaifin ya ce, dakin da shi da matarsa ke rayuwa a da kafin haihuwar 'yan hudun, yanzu ba ya isarsu.

"Ina neman agajin gwamna Babajide Sanwo-Olu na Legas, shugabannin kananan hukumomi uku na Badagry, da sauran masu hannu da shuni a fadin Najeriya don daukar nauyin 'ya'yan da aka haifa min.
"A halin yanzu, babban asibitin na bina makudan kudade, saboda sai da aka yi ma ta aiki sannan aka ciro yaran.
"Bani da wata kwakwkwarar sana'a, ina bukatar agaji daga 'yan Najeriya masu hannu da shuni don kula da 'yan huduna," a yadda yace.

Kara karanta wannan

Ya Yi Jiran Fiye Da Shekaru 50: Allah Ya Azurta Tsoho Mai Shekaru 83 Da Ɗa Na Farko

Wakilin NAN wanda ya ziyarci babban asibitin Badagry, ya ruwaito yadda Sekinat Abdullahi da 'yan hudunta suke sashin haihuwa na asibitin.

Olatunde Bakare, likitan da ya amshi haihuwar a asibitin, ya ce an haifi 'yan hudun tsakanin karfe 6:15 da 6:30 na daren Litinin.

A cewarsa, 'yan hudun- maza biyu da mata biyu na cikin koshin lafiya, amma a halin yanzu suna cikin kwalba a MCC.

Ya kara da bayyana yadda na karshe cikin 'yan hudun yake da kankanta, amma ana cigaba da basu kulawa ta musamman.

Sekinat, mai shekaru 26, mai sana'ar dinki, tayi godiya ga Ubangiji da kulawar da take samu daga asibitin har ta iya haifar 'yan hudun lafiya.

"Wannan ita ce haihuwata ta farko; ban taba sa ran 'yan hudu ba, amma ga shi sun zo duniya ta sanadi na.
"Ina so in yi amfani da wannan damar wajen neman agaji daga gwamnatin jihar Legas da mazauna Badagry da su kawo mana agaji, saboda ba zamu iya kula da 'yan hudun ba mu kadai.

Kara karanta wannan

London zuwa Legas a babur: 'Dan Najeriya ya kai Spain, ya ci nisan 702km daga 12,000km

"Nauyin zai wa mijina yawa shi kadai," a cewarta.

Bidiyon da hotunan auren fasto da 'yan mata 4 a rana 1, yace Injila ta bashi dama

A wani labari na daban, Zagabe Chiluza, fitaccen fasto ne daga gabashin Congo, ya bar mutane baki bude bayan ya auri mata hudu a rana daya duk da yana da mata daya da ya fara aure.

Faston da ya auri mata sama da daya, ya auri mata hudu duk 'yan mata, a wani bikin kece raini a shekarar da ta gabata.

Kamar yadda AfriMax sashin turanci suka ruwaito, mutumin ya saba wallafa hujjoji daga Injila don tabbatar da auren mace sama da daya ba zunubi bane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel