Matar aure ta sha da kyar, saurayinta ya nemi halakata yayi tsafi da ita

Matar aure ta sha da kyar, saurayinta ya nemi halakata yayi tsafi da ita

  • Funmilola Osundare matar aure ce da soyayya ta ja ta zuwa dakin saurayinta har tayi shirin kwana a GRA Akure, jihar Ondo
  • Sai dai a rashin saninta, saurayinta matsafi ne kuma tsakar dare ya nemi halakata inda ya sassare ta da adda
  • Ihunta da makwabtansa suka ji ne yasa suka gaggauta kiran Amotekun wadanda dirarsu ke da wuya saurayin ya cika bujensa da iska
  • A halin yanzu tana kwance rai a hannun Allah a asibitin koyarwa na jami'ar Akure kuma bata san inda kanta yake ba

Akure, Ondo - Wata matar aure, Funmilola Osundare ta sha da kyar, yayin da matsafin saurayinta yayi yunkurin halakata a Akure, babban birnin Ondo. Saurayinta wanda ba a bayyana sunansa ba, wanda ake zarginsa da zama matsafi yayi yunkurin halakata.

Kara karanta wannan

Ina alfahari da kai: Budurwar marigayi matukin jirgin NAF ta yi wallafa mai karya zuciya

Daukin da makwabta suka yi hanzarin kai wa wacce lamarin ya auku da ita ne ya tseratar da ita daga shekawa barzahu, yayin da makashin saurayinta ya yi kokarin halakata a wani gidan haya cikin Ijapo, GRA dake Akure.

Matar aure ta sha da kyar, saurayinta ya nemi halakata yayi tsafi da ita
Matar aure ta sha da kyar, saurayinta ya nemi halakata yayi tsafi da ita. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

An sami labarin yadda wacce lamarin ya auku da ita ta samu raunuka daban-daban a fuskarta, kafadunta da hannayenta, Legit.ng ta ruwaito.

Majiyoyi sun bayyana yadda saurayin nata, wanda 'dan wasan kwallon kafa ne ya kai matar gidan, inda ya koma ana kwanaki uku kafin aukuwar mummunan lamarin don ta debe masa kewa.

Legit.ng ta gano yadda wanda ake zargin ya kai ma ta hari a tsakiyar dare, amma kururuwar neman daukin da tayi ne ya janyo hankalin makwabta, wadanda suka gayyaci jami'an tsaro na Amotekun.

Kara karanta wannan

Kin jinin Musulmi: China ta yi Allah wadai da wadanda suka kona al-Qur'ani a Sweden

Wanda ake zargin ya ranta a na kare yayin da makwabta suka garzaya da wacce lamarin ya auku da ita asibitin 'yan sanda don neman lafiyarta, inda aka ki karbarta, gami da tura ta asibitin koyarwa na jami'ar likitanci dake Akure.

Bidiyo: Bayan shekara 20 da batan ta, mahaifiyar yara 8 ta dawo gida da kafafunta

A wani labari na daban, wasu 'ya'ya sun tsunduma cikin tsananin farinciki bayan an gano mahaifiyarsu Florence Ikhine, wacce ta bace a shekarar 2002 a Benin dake jihar Edo bayan kwashe shekaru 20 da bacewarta.

Princess Ehima Elema wacce ta sanar a shafinta na Facebook a shekarar 2019 cewa Florence, mahaifiyar yara takwas ta bace, ta sanar da dawowar mahaifiyar 'ya'ya takwas din.

Princess ta ruwaito yadda aka gano dattijuwar mai shekaru 68 a ranar Laraba, 20 ga watan Afirilu, 2022 wuraren titin Ehaekpen a Benin City dake Edo, inda daya daga cikin 'ya'yanta ke zama.

Kara karanta wannan

Kyawawan hotunan 'dan tsohon gwamna yana mika bukatar aure ga budurwarsa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel