Ya Yi Jiran Fiye Da Shekaru 50: Allah Ya Azurta Tsoho Mai Shekaru 83 Da Ɗa Na Farko

Ya Yi Jiran Fiye Da Shekaru 50: Allah Ya Azurta Tsoho Mai Shekaru 83 Da Ɗa Na Farko

  • Sai da Mzee Yosia Mwesigye ya yi jiran shekaru 57 kafin Ubangiji ya azurta shi da da, har ta kai ga matarsa ta farko ta mutu ba ta haihu ba
  • Dattijon ya tsare kansa a wurin marigayiyar matarsa ba tare da bin wasu matan ba, kuma bai taba danasanin rashin haihuwar ba
  • Mwesigye ya auri masoyiyarsa, Jane Tukamuhabwa wacce ta rasu a ranar 25 ga watan Afiriln 1962 a lokacin yana da shekaru 23 da haihuwa
  • Lokacin da suka je asibitoci, an sanar da su cewa zasu iya haihuwa, amma a shekarar 2005, aka gano Tukamuhabwa tana da dajin mahaifa, daga baya ta mutu

Uganda - Wani dattijo mai shekaru 83 da haihuwa dan kasar Uganda ya shiga farin ciki bayan ya samu haihuwa yayin da ya kai shekaru 79 haihuwa ba tare da ya taba haihuwa ba.

Kara karanta wannan

Kin jinin Musulmi: China ta yi Allah wadai da wadanda suka kona al-Qur'ani a Sweden

Mzee Yosia Mwesigye ya yi jiran tsawon shekaru 57 amma bai taba samun haihuwa ba daga tsohon auren da ya yi. Sai dai bai yi danasanin yadda marigayiyar matarsa ta gaza haihuwa ba.

Ya Yi Jiran Fiye Da Shekaru 50: Ubangiji Ya Azurta Tsoho Mai Shekaru 83 Da Ɗa Na Farko
Mzee Yosia Mwesigye a tsakiya yana rike da dansa na fari. Hoto: Daily Monitor.
Asali: UGC

A wani rahoto na Daily Monitor, an ga yadda mutumin ya auri masoyiyarsa, Jane Tukamuhabwa (marigayiya) a ranar 25 ga watan Afirilun 1962, yayin da ya ke da shekaru 23.

Amma sun kasa haihuwa ko daya. Kamar yadda ya ce:

“Lokacin da muka kai ziyara asibitoci, sun sanar da mu cewa duk lafiyarmu kalau.”

Ya ci gaba da tsare kansa a wurin matarsa bayan likita ya ba su tabbacin lafiyarsu.

Sai dai a 2005, an gano cewa Tukamuhabwa tana da cutar dajin mahaifa inda ta rasu a shekarar 2018.

Kara karanta wannan

Kyawawan hotunan 'dan tsohon gwamna yana mika bukatar aure ga budurwarsa

Ya ci gaba da cewa:

“Mun yi iyakar kokarinmu amma abin ban takaicin shi ne yadda ta mutu ba tare da mun haihu ba.”

Rayuwa da ma’aikata tare da rike yara

Mwesigye ya ce ya yi rayuwa da ma’aikata yayin da suka rike yara bayan mutuwar matarsa amma suna kwana ne a dakin kwanan yara maza yayin da ya ke kwana shi daya a cikin dakinsa, rahoton GhanaWeb.

A lokacin ne rayuwa ta sauya masa inda ya fara tunanin kara aure. Mwesigye ya kara aure lokacin yana da shekaru 79 da haihuwa.

Bayan kwanaki kadan ‘yar uwar Mzee Mwesigye ta kawo masa mata har gida daga nan ya aure ta.

Ya kara da cewa:

“Na yi matukar farin ciki har sai da na yi kuka da hawaye sannan na sa wasu ma’aikatana su yanka akuya. Haka na samu auren wata matar, Sharon Arinaitwe.”

Haihuwar jaririnsu

Kara karanta wannan

Daga Landan zuwa Lagas: 'Yan Najeriya 3 da suka yi tafiyar ban mamaki a kafa da babur

Bayan shekaru biyu da aurensa da Arinaitwe, wacce yanzu shekarunta 29, ta sanar da shi cewa ta samu ciki. A ranar 23 ga watan Maris, ma’aikatan asibiti da ke North-Kigezi Health IV Rugarama suka amshi haihuwar jaririnsu.

Ina matukar farin ciki da Ubangiji ya nuna min da na a wannan shekarun nawa. Ban taba tunanin zan haihu ba, amma na dade ina addu’o’i wadanda yanzu Ubangiji ya amsa.

Ya ce abinda ya fi komai radadi shi ne mutuwa babu da, don da shi ne kadai ake tuna mutum.

Tsoho mai shekaru 84 da ya bar gida tsawon shekaru 47 ya dawo, ya nuna ɓacin ransa don matansa 2 sun sake aure

A wani labarin daban, wani tsoho mai shekaru 84, Peter Oyuk ya sha mamakin yadda matan sa 2 suka sake aure bayan ya yi tafiya tsawon shekaru 47.

Kamar yadda LIB ta ruwaito daga The Standard, mutumin ya bar kauyen Makale dake Malava bangaren Kakamega a shekarar 1974 lokacin yana da shekaru 37.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda fasinja ta yanke jiki ta fadi, tace ga garinku a filin jirgin sama dake Abuja

Ya sanar da iyalan sa cewa ya tafi neman arziki don tallafa wa matan sa 2 da yaran sa 5 duk da dai bai sanar da su lokacin da zai dawo ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel