Bidiyon da hotunan auren fasto da 'yan mata 4 a rana 1, yace Injila ta bashi dama

Bidiyon da hotunan auren fasto da 'yan mata 4 a rana 1, yace Injila ta bashi dama

  • Wani fasto 'dan Jamhuriyar Congo, Zagabe Chiluza ya auri mata hudu, duka 'yan mata, bayan wasu 'yan watanni da yin bikin kece raini a gabashin Congo
  • Ya fara auren matarsa ta farko kafin ya auri mata hudun, tare da cewa ya samu halascin auren mace sama da daya daga littafin Injila, tare da kafa misali da Jacob
  • Faston ya ce maza daga majami'arsa 'yan mata kadai suke aura, inda ya bai wa saura karfin guiwar auren mace sama da guda daya

Zagabe Chiluza, fitaccen fasto ne daga gabashin Congo, ya bar mutane baki bude bayan ya auri mata hudu a rana daya duk da yana da mata daya da ya fara aure.

Faston da ya auri mata sama da daya, ya auri mata hudu duk 'yan mata, a wani bikin kece raini a shekarar da ta gabata.

Kara karanta wannan

Sarkin mawaka ko sarkin hauka - Babanchinedu ya yiwa naziru wankin babban bargo kan Nafisa Abdullahi

Kamar yadda AfriMax sashin turanci suka ruwaito, mutumin ya saba wallafa hujjoji daga Injila don tabbatar da auren mace sama da daya ba zunubi bane.

Bidiyon auren fasto da 'yan mata 4 a rana 1, yace Injila ta bashi dama, matansa 5 yanzu
Bidiyon auren fasto da 'yan mata 4 a rana 1, yace Injila ta bashi dama, matansa 5 yanzu. Hoto daga Afrimax
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Dama can ina da mata daya, kuma a yau zan auri wadannan hudun. Za su hadu da matata ta farko," a cewarsa
"Jacob ya auri mata da yawa, Leah da Rachel, sai Bilha da Zilpa. Mata hudu na mutum daya," a cewarsa.

Bidiyon auren fasto da 'yan mata 4 a rana 1, yace Injila ta bashi dama, matansa 5 yanzu
Bidiyon auren fasto da 'yan mata 4 a rana 1, yace Injila ta bashi dama, matansa 5 yanzu. Hoto daga Afrimax
Asali: UGC

Zagabe ya ce ya gano hakan ne a 1986, sannan lokacin bikin auren, yayin jawabi ga baki, ya ce; "Ina farin cikin mallakar mata biyar."

Mata hudun da Zagabe ya aura duk 'yan mata ne a lokacin da ya auresu a majami'arsa cikin gabashin Congo.

Wasu mambobin majami'arsa sun amince da maganarsa cewa, Injila ta talasta auren mata sama da daya.

Kara karanta wannan

Matar da ta fi kowacce mace kudi a Najeriya ta bukaci mata da su mika wuya ga mazajensu

AfriMax sun kai wa faston ziyara, tare da matansa a gidansu, kuma suna zaune cikin farin ciki.

Bidiyon auren fasto da 'yan mata 4 a rana 1, yace Injila ta bashi dama, matansa 5 yanzu
Bidiyon auren fasto da 'yan mata 4 a rana 1, yace Injila ta bashi dama, matansa 5 yanzu. Hoto daga Afrimax
Asali: UGC

Allah ya yi min baiwar auren kyawawan mata, Salon sace zuciyar 'yan mata daga bakin Alaafin yayin rayuwarsa

A wani labari na daban, Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi lll, ya riski magabatansa a daren Juma'a, wanda hakan ya kawo karshen shekaru 52 da ya yi a karagar mulki.

Oba Adeyemi, mai shekaru 83, wanda ya rasu a asibitin koyarwa na jami'ar Afe Babalola na Ado Ekiti dake jihar Ekiti, shine Alafin na Oyo da yafi kowanne basarake dadewa a karagar mulki.

Ya rasu ya bar mata 11, uwar gidan mai suna Ayaba Abibat Adeyemi, wacce yafi zuwa da ita taruka ko daya daga cikin sauran matayen nashi guda goma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel