Yajin aiki: Gwamnatin Buhari ta dauki matakin tsayar da albashin lakcarori
- Ana zargin gwamnatin tarayya da kin biyan albashi da alawus din malaman jami’o’i da ma’aikata na watan Maris
- Shugaban kungiyar malaman jami'a ta NAAT, Ibeji Nwokoma ne ya bayyana wannan zargi kan gwamnatin Najeriya
- Nwokoma ya tabbatar da cewa ba a biya ‘ya’yan kungiyarsa cikakken albashinsu na watan Maris da gwamnati ta biya kwananan ba
Najeriya - Alamu na nuni da cewa watakila gwamnatin tarayya ta aiwatar da manufar ‘ba aiki, ba albashi’ domin dakile yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta dade tana yi.
Vanguard ta ruwaito cewa matakin da gwamnati ta dauka ya biyo bayan sanarwa da wasu wasiku da hukumar da ke yajin aikin ta aikewa da wasu kungiyoyin jami’o’in da suka hada da kwamitin hadin gwiwa na JAC wanda ya kunshi NASU da SSANU.
Majiyoyin da suka yi magana kan lamarin sun ce gwamnatin Najeriya ta yi amfani da manufar tsayar da albashin ne a watan Maris din 2022.
Shugaban NAAT, Ibeji Nwokoma wanda ya tabbatar da lamarin ya ce ba a biya mambobin kungiyarsa cikakken albashin su na watan Maris ba.
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Nwokoma ya kuma zargi FG da yin watsi da duk wasu takardu da wasiku da aka aika na neman magance matsalolin da kungiyar ta bijiro dasu.
A cewar Nwokoma, maimakon gwamnatin Najeriya ta gayyaci ma’aikatan da ke yajin aikin domin tattaunawa a kan lamarin, sai kawai ta aiwatar da manufofinta na ‘ba aiki, ba albashi’.
Ba za mu yi kasa a gwiwa ba
Ya kuma kara da cewa mambobin kungiyar ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen neman ingantaccen yanayin aiki ga ma’aikata da dalibai ba.
Kalamansa:
“Yau, mun shiga mako na biyar na yajin aikin gargadi, makwanni biyu na farko, sannan muka kwashe makwanni hudu.
“Abin takaici, kamar yadda muke magana, gwamnati ba ta kula da duk sanarwar yajin aikin ba da duk wasikun da muka rubuta musu har yau.
“Har ila yau, gwamnati ba ta gayyace mu ba, ko kuma ta ga ya dace ta gayyace mu wajen tattaunawa a kan teburi, domin a samo mafita ba.
"Kuma abin takaici, sai kawai gwamnati ta yanke shawarar dakatar da albashin mu, ta hanyar amfani da tsarin ba aiki, ba albashi.”
Wakilin Legit.ng Hausa ya nemi jin ta bakin wasu malamai daga jami'o'in jiha na Gombe, Bauchi da Taraba, inda na Gombe da Taraba suka tabbatar da rashin samun albashin watan Maris da ta gabata.
Shi kuwa na jami'ar jihar Bauchi, ya ki amsa tambayar, inda yace:
"Aikina tsakani na ne da gwamnati, don haka ba zan iya cewa komai akai ba."
A bangare guda, wani malamin jami'ar tarayya da ke Kashere a jihar Gombe da ya nemi a sakaya sunansa saboda ba aikinsa kariya ya ce:
"Tun da na fara aiki shekaru uku ban taba samun irin wannan ba, tun da aka fara biya na ina samun albashi kan lokaci. Watan Maris ni da abokai da yawa mun koka kan rashin albashi, amma ba mu da tabbacin hakan na da nasaba da yajin aiki.
Shi ma wani ma'aikacin jami'ar tarayya da ke Lafia a jihar Nasarawa, ya ce yana jiran tsammani, ga kuma Afrilu ta kare.
Ku Ba Mu N200m Cikin Kuɗin Tallafin Man Fetur, Mu Koma Aji: ASUU Ta Roƙi Gwamnatin
A baya, Shugaban Kungiyar malaman jami’o’i masu koyarwa, ASUU, Farfesa Emmanuel Osedeke ya ce gwamnatin tarayya har yanzu tana nuna halin ko-in-kula akan yajin aikin ASUU wanda hakan ya sa daliban jami’o’in Gwamnatin Najeriya suke zaune a gidajensu, rahoton The Punch.
A cewarsa, gwamnati ta kawo mafita akan kudin tallafin man fetur da kasafin Naira tiriliyan 4 amma kuma har yanzu bata ce komai ba akan ilimin jami’o’inta.
Farfesa Osodeke ya ce Naira biliyan 200 gwamnati za ta cire daga kudin kasafin tallafin man fetur, Naira Tiriliyan 4, sannan ta samu rarar Naira Tiriliyan 3.8 wurin kawo karshen matsalolin jami’o’i, Channels Television ta rahoto.
Asali: Legit.ng