Martanin yan Najeriya kan sabuwar wakar rashin tsaro da mawakin Buhari, Rarara ya yi

Martanin yan Najeriya kan sabuwar wakar rashin tsaro da mawakin Buhari, Rarara ya yi

  • Yan Najeriya sun tofa albarkacin bakunansu bayan bayyanar sabuwar wakar da Kahutu Rarara ya yi a kan matsalar tsaro
  • Da dama na ganin abun da mawakin ya yi butulci ne tsantsa ganin cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na shirin zuwa karshe
  • Wasu kuma na ganin dabara ce Rarara yake yi domin samun tudun dafawa ta yadda za a dama da shi a zaben 2023

Yan Najeriya sun caccaki shahararren mawakin nan na shugaban kasa Muhammadu Buhari da manyan yan siyasar arewa, Daudu Kahutu Rarara, kan sabuwar wakar da ya yi na sukar gwamnati kan tsaro.

Mawaki Rarara ya yi kaurin suna wajen wakewa da yabon Buhari, kuma yana kan gaba cikin wadanda suka yi masa kamfen don ganin ya zarce a kan kujerarsa a 2019.

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar APC ta hana Amaechi, Ngige, Malami da wasu Ministoci yin takara

Martanin yan Najeriya kan sabuwar wakar rashin tsaro da mawakin Buhari, Rarara ya yi
Martanin yan Najeriya kan sabuwar wakar rashin tsaro da mawakin Buhari, Rarara ya yi Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Saboda haka ne ma shugaban kasar ya nada shi a matsayin shugaban mawakarsa.

Sai dai kuma mutane da dama sun cika da mamaki a lokacin da suka wayi gari da wakarsa wacce ta bayyana a shafukan sada zumunta inda a ciki yake kalubalantar gwamnati a kan rashin baiwa al’ummar kasar cikakken tsaro.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Harma a cikin baitin wakar tasa ya bayyana cewa yan kadan ne ke yiwa gwamnatin Buhari uzuri a yanzu saboda ta gaza kare kasar, inda yace ana jin wai-wai a da amma ga shi abun ya bayyana a zahiri.

Tuni dai yan Najeriya suka fito suka yi sharhi kan lamarin, inda da dama ke ganin mawakin na kokarin samun wani tudun dafawa ne duba ga cewar wa’adin wannan gwamnati na gab da karewa.

Legit Hausa ta duba shafinta na Facebook inda ta zakulo martanin wasu daga cikin mabiyanta kan haka.

Kara karanta wannan

Mawaki Rarara ya yiwa shugaban kasa Buhari wankin babban bargo a sabuwar wakarsa

Ibrahim Aliyu ya yi martani:

“Shege dan iska,ya ga gwamnatin ta zo karshe bari yayi waje dasu ya sake duban wanda zai bi, bambadanci bai yi ba.”

Muhammad Usman Muallah ya ce:

“Shege rarara gaskiya babu butulu kamar mawaƙi, ko uwar ku ɗaya idan tenure ta ƙare sai ya caccake ka.”

Akans Ayinde ya yi martani:

“Yo dama kudin da muka tara masa duk shirin wakan sallamar Baba ne? Toh Allah ya fi ka.”

Hassan Suleiman Moriki ya ce:

“Dan iskan banza tunda sunkai yan arewa ga maganar banza kuma mulki ya kare ai dole yayi butulci. Munafukin banza mabaraci, yanzu kuma wani zai kama wanda zai gurgura.”

Adamu Yusha'u Kainuwa ya ce:

“Ai yaga mulkin yazo karshe shine zai chanza inuwa muma yanzu mun gano gaskiya”

Annoor Yero ya ce:

“Ya makara dan mother ɗinsa. Bashi ya tunzura ƴan Arewa suka zaɓo mana lusarin shugaba ba. Allah Ya isanmu akanku duka.”

Kara karanta wannan

Shirin 2023: kwamishinan gwamna Zulum ya yi murabus, zai tsaya takara kujerar yankinsu

Ibraheem Abubakar Funkieez ya yi martani:

“Tunda mulkinshi yakareba yasan bazaikara samun kudi gurnshiba Za a Koma gurin Wani Ai tun a Kan Kwankwaso yanunamana Shi yaye.”

Rabiu Shehu ya yi martani:

“Ka ji shege, kaska, Marar mutunci. Duk za mu yi maganinsu har tsofon da juyawa bayanma.”

Mawaki Rarara ya yiwa shugaban kasa Buhari wankin babban bargo a sabuwar wakarsa

Mun kawo a baya cewa shahararren mawakin nan na siyasa wanda ya yi suna wajen wake shugaban kasa Muhammadu Buhari da wasu manyan yan siyasar arewa, Dauda Kahutu Rarara, ya magantu kan gazawar gwamnati mai ci a wata sabuwar waka.

A cikin wakar, Rarara ya jagoranci wata tawaga ta shahararrun mawakan Hausa karkashin 13X13, wata kungiya ta masana’antar Kannywood.

Lamarin ya haifar da zazzafan martani kan ko babban dan kashenin Buharin baya tare da shi kuma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng