Yan bindiga sun kashe Kwamandan Yan Banga, sun tarwatsa mutanen gari a Zamfara

Yan bindiga sun kashe Kwamandan Yan Banga, sun tarwatsa mutanen gari a Zamfara

  • Yan bindiga sun kai hari ƙauyen Mada dake ƙaramar hukumar Gusau jihar Zamfara domin ɗaukar fansa
  • Mazauna garin sun bayyana cewa yan ta'addan sun kashe shugaban yan Bijilanti da wasu dakarunsa guda shida a harin
  • Rahoto ya nuna cewa mutanen garin sun bar gidajensu saboda tsoron abinda ka iya zuwa ya dawo daga yan ta'addan

Zamfara - Mazauna ƙauyen Mada a ƙaramar hukumar Gusau ta jihar Zamfara sun gudu sun bar gidajen su saboda tsoron harin ta'addancin yan bindiga.

Hakan na zuwa ne biyo bayan kashe Yan Sa'akai guda Bakwai a wani hari da mutane ke tunanin yan bindiga sun kaddamar domin ɗaukar fansa.

Da suke tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Premium Times, hukumomin yan sanda sun bayyana cewa tuni aka kara jibge dakaru a ƙauyen domun kare lafiyar mutane.

Kara karanta wannan

Ruwan Zuma: An kashe mutum uku kan wata tsaleliyar budurwa a jihar Kwara

Yan bindiga sun sake kai hari Zamfara
Yan bindiga sun kashe Kwamandan Yan Banga, sun tarwatsa mutanen gari a Zamfara Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Yusuf Anka, wani mazauni da ya san tushen rikicin dake faruwa a yankin, ya ce kwamandan yan Bijilanti, Dan-Mudi Na Mada, ya jagoranci dakarunsa zuwa maɓoyar yan bindiga, suka sheƙe gawutaccen ɗan bindiga 'Mala’ikan Hausawa'.

Anka ya ƙara da cewa wannan kisan da aka yi wa yan bindiga ya fusata su, har ta kai ga suka kawo harin ɗaukar fansa.

Ya ce:

"Tawagar Ɗan-Mudi ta yi nasarar sheƙe gawurtaccen ɗan bindiga da ake kira Mala'ikan Hausawa, haka nan kuma an zarge shi da ƙona Rugar fulani a Tsafe."

Yusuf anka ya bayyana cewa marigayi shugaban yan Banga ya sha yabo kan kokarin kare ƙauyukan Hausawa musamman Mada da Wonaka, amma ana zarginsa da hannu a kisan Fulani da ba ruwansu a yankin.

Yadda lamarin ya faru

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wasu yan bindiga sun saki sabon Bidiyo, sun yi barazanar hana zaɓen 2023

Wata majiya a ƙauyen da abun ya faru, da ya nemi a sakaya sunansa saboda tsaro, ya ce yan ta'addan sun farmaki yan Bangan ne da ƙarfe 10:47 na dare.

"Yan bindigan sun yi yunkurin kwace iko da ƙauyen Mada amma suka fuskanci tirjiya daga Yan Bijilanti, sun kwashe awanni ana musayar wuta daga bisani suka ci ƙarfin Yan Bijilanti, suka kashe mutum 7."
"Duk da haka ba su ci nasarar shiga cikin gari ba biyo bayan isowar Sojoji da kuma Dakarun yan sanda. Bamu san me zai faru ba saboda za su iya dawowa."

Rahotanni sun nuna cewa mafi yawan mutanen garin sun tattara kayan su, sun bar kauyen domin tsira da rayuwarsu.

A wani labarin kuma Rikicin APC a Kano: Sanata Shekarau ya yi magana kan batun ficewa daga jam'iyyar APC

Tsohon gwamnan Kano, Mallam Ibrahim Shekarau, ya musanta rahoton da ke yawo cewa yana shirin barin APC.

Kara karanta wannan

Jirgin yaƙin Sojojin Najeriya ya yi luguden wuta kan kananan yara bisa kuskure a jihar Neja

Shekarau mai wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar Dattawa ya ce da su aka yanke wa APC cibiya, yanzun suna dakon hukuncin Kotun ƙoli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel