Jirgin yaƙin Sojojin Najeriya ya yi luguden wuta kan mutane bisa kuskure, rayuka sun salwanta

Jirgin yaƙin Sojojin Najeriya ya yi luguden wuta kan mutane bisa kuskure, rayuka sun salwanta

  • Jirgin yaƙin sojin NAF ya yi kuskuren kashe kananan yara da dama a kauyen Kurebe dake yankin Shiroro, jihar Neja
  • Wani bawan Allah da lamarin ya rutsa da ƴaƴansa mata biyu da jikoki, ya ce wannan ba shi ne karo na farko ba
  • Kakakin gamayyar ƙungiyoyin al'umma na yankin, Salis Sabo, shi ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba

Niger - Wani jirgin yaƙin rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) dake aikin kakkabe yan ta'adda ya yi kuskuren kashe kananan yara shida a jihar Neja.

Lamarin ya faru ne a ƙauyen Kurebe dake ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Neja ranar 13 ga watan Afrilu, 2022.

Jaridar The Cable ta gano cewa yankin ya jima cikin halin zaman ɗar-ɗar da rashin tabbas, saboda yawan hare-haren yan ta'adda.

Kara karanta wannan

Bayan gana wa da Buhari, Gwamnan APC ya fallasa yadda yan siyasa ke ɗaukar nauyin yan bindiga a Najeriya

Jirgin yaƙin Sojojin Najeriya.
Jirgin yaƙin Sojojin Najeriya ya yi luguden wuta kan mutane bisa kuskure, rayuka sun salwanta Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Kakakin gamayyar ƙungiyoyin yankin (COSA), Salis Sabo, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sabo ya yi bayanin cewa jirgin ya yi kuskuren taɓa kananan yaran ne lokacin da suke kan hanyar komawa gida daga wurin da suke zuwa ɗebo ruwa a yankin.

Ya makusantan yaran suka ji da lamarin?

Ya ƙara da cewa biyu daga cikin yaran da lamarin ya shafa marayu ne, waɗan da iyayen su suka mutu a wani harin da yan bindiga suka kawo ƙauyen.

Aminiya ta rahoto Sabo ya ce:

"Wani bawan Allah da ya rasa ƴaƴansa na ciki biyu da jikokinsa a lamarin, ya ce babu wani ɗan bindiga a ƙauyen ko guda ɗaya a lokacin da Jirgin yaƙin ya bude wa kananan yaran wuta."
"Maɓoyar yan bindigan yankin sananne ne, sun kasu zuwa kashi biyu, kowace tawaga da sansanin su, ɗaya na haɗewa da kauyen daga Unguwan Zomo, ɗayar kuma daga Kwantan Yashi."

Kara karanta wannan

Mutanen dake ɗaukar nauyin yan bindiga a jihata, Gwamnan APC ya fasa kwai

"Dan haka ba bu dalilin da zai sa jirgin yaƙi kawo hari ƙauyen su, kuma wannan shi ne karo na biyu da irin haka ta faru a ƙauyen."

A wani labarin kuma Mataimakin Kwamishinan Yan Sanda Ya Yanke Jiki Ya Faɗi, Ya Mutu Yana Tsaka da Aiki a Ofis

Mataimakin kwamishinan yan sanda na jihar Bayelsa mai kula da sashin shugabanci ya rasu yana cikin aiki a Hedkwata.

Rahoto ya nuna cewa Mamacin ya yanke jiki ya faɗi a cikin Ofishinsa, aka yi kokarin kai shi Asibiti amma rai ya yi halinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel