Yan bindiga sun sace makiyaya 10 da shanu 300 a jihar Anambra

Yan bindiga sun sace makiyaya 10 da shanu 300 a jihar Anambra

  • Masu garkuwa da mutane sun sace mambobin kungiyar Makiyaya ta Najeriya (MACBAN) guda 10 da shanayensu 300 a jihar Anambra
  • Sun farmaki rugar makiyayan da ke Obene a karamar hukumar Ogbaru ta jihar a ranar Asabar, 23 ga watan Afrilu
  • Yan bindigar sun tuntubi yan uwan mutanen da suka sace sannan sun nemi a biya kudin fansa naira miliyan 4

Anambra - Wasu yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da mambobin kungiyar Miyetti Allah guda 10 a yankin karamar hukumar Ogbaru da ke jihar Anambra.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa lamarin ya afku ne a rugar makiyaya da ke garin Obene a ranar Asabar, 23 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun hallaka jami’an yan sanda 3 a wani farmaki da suka kai ofishinsu a Kogi

An kuma tattaro cewa maharan sun sace kimanin shanaye guda 300 mallakar makiyayan.

Yan bindiga sun sace makiyaya 10 da shanu 300 a jihar Anambra
Yan bindiga sun sace makiyaya 10 da shanu 300 a jihar Anambra Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Jaridar The Nation ta rahoto cewa maharan sun tuntubi yan uwan mutanen da aka sace sannan sun bukaci a biya naira miliyan 4 a matsayin kudin fansarsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake martani kan lamarin, kakakin yan sandan Anambra, Tochukwu Ikenga, ya bayyana cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da ganin cewa an gurfanar da maharan.

Ya ce:

“Zan iya baku tabbacin cewa rundunar yan sandan jihar Anambra, karkashin jagorancin kwamishina, CP Echeng, za ta tabbatar da ganin an ceto mutanen da aka sace sannan a sadasu da yan uwansu cikin koshin lafiya.

“Na kira sarkin biyo bayan samun sakon da ya aike mani kuma na bukace shi da ya je ofishin yan sanda mafi kusa da shi sannan ya shigar da kara. Wannan zai bamu damar fara bincike, tunda ya yi ikirarin cewa maharan sun kira iyalan.

Kara karanta wannan

Miyetti Allah: Ƴan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Mambobinmu 10 Da Shanu 300, Sun Buƙaci N4m Da Bindiga Ɗaya a Anambra

“Wannan zai ba yan sandan damar yin bincike da kyau da kuma kaddamar da aikin ceto mutanen.”

‘Yan sandan Abuja sun kai samame kan tsaunuka, sun fatattaki ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane

A wani labarin, rundunar yan sandan babbar birnin tarayya Abuja sun fara kai samame kan tsaunukan da ke yankin.

Jaridar Punch ta rahoto cewa masu fashi da makami, masu garkuwa da mutane da sauran miyagu da suka addabi birnin tarayya, musamman a garuruwan kan iyaka, suna gina sansaninsu ne a kewayen tsaunuka a Abuja.

Rundunar da ke aiki kan bayanan sirri ta kai samame kan tsaunukan sannan ta lalata mafakar masu garkuwa da mutane a yankin Kwali da ke birnin tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng