Yan bindiga sun hallaka jami’an yan sanda 3 a wani farmaki da suka kai ofishinsu a Kogi

Yan bindiga sun hallaka jami’an yan sanda 3 a wani farmaki da suka kai ofishinsu a Kogi

  • Wasu yan bindiga sun kashe jami’an yan sanda uku a safiyar ranar Asabar a jihar Kogi yayin da su ka kai hari ofishinsu
  • Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, William Ovye-Aya, ya tabbatar da afkuwar mummanan al’amarin
  • Tuni a ka tura jami'ai domin bin sahun maharan da nufin kamo su da kuma gurfanar da su a gaban alkali

Kogi - Wasu yan bindiga da ake zaton masu fashi da makami ne sun farmaki ofishin yan sandan Adavi da ke jihar Kogi a safiyar ranar Asabar, 23 ga watan Afrilu, sun kashe yan sanda uku.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Kogi, William Ovye Aya, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya saki a Lokoja, a ranar Asabar, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun Tabbatar Da Kisan Mutum 10 Da Boko Haram Suka Yi a Geidam

Yan bindiga sun hallaka jami’an yan sanda 3 a wani farmaki da suka kai ofishinsu a Kogi
Yan bindiga sun hallaka jami’an yan sanda 3 a wani farmaki da suka kai ofishinsu a Kogi Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Ya ce:

“Rundunar ta samu rahoton mummunan lamarin da ya afku a ofishin yan sanda na Adavi, inda wasu yan iska suka farmaki ofishin daga daya bangaren suna ta harbi kan mai uwa da wabi, amma jami’an mu da jami’an sashin gaggawa da ke gudanar da ayyuka na musamman a karamar hukumar suka maida martani.”

Ya ce rundunar ta rasa jami’anta uku a yayin musayar wuta sannan ‘yan bindigar sun gudu da raunukan harbin bindiga saboda sun kasa shiga ofishin.

Aya ya ce kwamishinan yan sandan jihar, CP Edward Egbuka, ya tura jami'ai domin dawo da zaman lafiya a yankin, tare da bin sahun barayin da nufin kama su da kuma gurfanar da su gaban kotu.

Rundunar ta yi kira ga al’umman Adavi da sauran garuruwa da su zuba ido sannan su kawo rahoton duk wani da suka gani da raunin harbi zuwa ofishin yan sanda mafi kusa da su, rahoton Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Tsohon na kusa da Buhari ya fice daga jam'iyyar APC, ya jero dalilai

Katsina: 'Yan sanda sun halaka 'yan ta'adda 2, sun ceto wasu da aka yi garkuwa da su

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta yi nasarar sheke a kalla 'yan ta'adda guda biyu, tare da gano makamansu, kayan sihirce-sihircensu da abubuwa masu fashewa a ranar Alhamis.

Channels TV ta ruwaito cewa, kakakin 'yan sandan, Gambo Isah, ya sanar da hakan yayin tattaunawa da manema labarai a hedkwatar rundunar a Katsina.

Ya ce, an yi nasarar sheke 'yan ta'addan bayan samun wani kiran gaggawa da rundunar tayi na cewa 'yan bindiga sun kai wa kauyen Tsamiyar Gamzako dake karamar hukumar Kafur na jihar hari, gami da yin garkuwa da wata mata mai shekaru 30 da 'diyarta 'yar watanni 15.

Asali: Legit.ng

Online view pixel