‘Yan sandan Abuja sun kai samame kan tsaunuka, sun fatattaki ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane
- Yan sanda a babbar birnin tarayyar kasar sun kai samame kan tsaunuka da ke Abuja domin fatattakar miyagu
- A yanzu haka, jami'an rundunar sun farmaki mafakar masu garkuwa da mutane a yankin Kwali inda suka lalata sansanin su
- Yan sandan wadanda suka kakkabe tsaunukan Yangoje da Old Chukuku sun sha alwashin ganin bayan duk wasu miyagu da suka addabi birnin da kewayenta
Abuja - Rundunar yan sandan babbar birnin tarayya Abuja sun fara kai samame kan tsaunukan da ke yankin.
Jaridar Punch ta rahoto cewa masu fashi da makami, masu garkuwa da mutane da sauran miyagu da suka addabi birnin tarayya, musamman a garuruwan kan iyaka, suna gina sansaninsu ne a kewayen tsaunuka a Abuja.
Rundunar da ke aiki kan bayanan sirri ta kai samame kan tsaunukan sannan ta lalata mafakar masu garkuwa da mutane a yankin Kwali da ke birnin tarayya.
Ta ce zuwa yanzu yan sanda sun kakkabe masu laifi daga tsaunuka a Yangoje da Old Chukuku.
Mataimakin kwamishinan yan sanda da ke kula da ayyukan, Ben Igwe, ya ce za a ci gaba da aikin har sai an fitar da dukkanin miyagu daga birnin.
Yan bindiga sun hallaka jami’an yan sanda 3 a wani farmaki da suka kai ofishinsu a Kogi
A wani labarin kuma, wasu yan bindiga da ake zaton masu fashi da makami ne sun farmaki ofishin yan sandan Adavi da ke jihar Kogi a safiyar ranar Asabar, 23 ga watan Afrilu, sun kashe yan sanda uku.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Kogi, William Ovye Aya, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya saki a Lokoja, a ranar Asabar, Daily Trust ta rahoto.
Ya ce rundunar ta rasa jami’anta uku a yayin musayar wuta sannan ‘yan bindigar sun gudu da raunukan harbin bindiga saboda sun kasa shiga ofishin.
Asali: Legit.ng