Allah ya yi min baiwar auren kyawawan mata, Salon sace zuciyar 'yan mata daga bakin Alaafin yayin rayuwarsa

Allah ya yi min baiwar auren kyawawan mata, Salon sace zuciyar 'yan mata daga bakin Alaafin yayin rayuwarsa

  • Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi, ya rasu yana da shekaru 83 a asibitin koyarwa na jami"ar Afe Babalola na Ado Ekiti
  • Kamar yadda ratotannin dake yawo a yanar gizo suka bayyana, marigayin basaraken Oyo, ya rasu ya bar kyawawan mata da dama
  • Marigayin basaraken Oyo, yayin wata tattaunawa kafin mutuwarsa, ya bayyana yadda yake mu'amala da matayensa masu yawa

Oyo, Ibadan - Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi lll, ya riski magabatansa a daren Juma'a, wanda hakan ya kawo karshen shekaru 52 da ya yi a karagar mulki.

Oba Adeyemi, mai shekaru 83, wanda ya rasu a asibitin koyarwa na jami'ar Afe Babalola na Ado Ekiti dake jihar Ekiti, shine Alafin na Oyo da yafi kowanne basarake dadewa a karagar mulki.

Allah ya yi min baiwar auren kyawawan mata, Salon sace zuciyar 'yan mata daga bakin Alaafin yayin rayuwarsa
Allah ya yi min baiwar auren kyawawan mata, Salon sace zuciyar 'yan mata daga bakin Alaafin yayin rayuwarsa. Hoto daga Authentic Voice
Asali: Twitter

Marigayin basaraken ya rasu ya bar mata da dama

Kara karanta wannan

Sarkin Oyo ya hango mutuwarsa, ya fada mana cewa magabatansa sun yi kira - Hadimarsa

Ya rasu ya bar mata 11, uwar gidan mai suna Ayaba Abibat Adeyemi, wacce yafi zuwa da ita taruka ko daya daga cikin sauran matayen nashi guda goma.

Sauran matanshi sun hada da: Ayaba Rahmat Adedayo Adeyemi, Ayaba Mujidat Adeyemi, Ayaba Rukayat Adeyemi, Ayaba Folashade Adeyemi, Ayaba Badirat Ajoke Adeyemi, Ayaba Memunat Omowunmi Adeyemi, Ayaba Omobolanle Adeyemi, Ayaba Moji Adeyemi, Ayaba Anuoluwapo Adeyemi, And Ayaba Damilola Adeyemi.

Yayin magana game da aurensa, a lokacin rayuwarsa, marigayin basaraken a daya daga cikin zantawar da akai dashi, ya bayyana yadda yake kaunar dukkan Oloris dinsa (matansa), da kuma yadda yake mu'amala dasu.

Kamar yadda City People ta nuna, ya ce: "Ban nemi auren daya daga cikin matana ba. Su suka zabi rayuwa dani, saboda ina turasu makaranta. Bayan sun gama jami'a, na ce dasu su tafi, amma suka ki, sannan suka tsaya akan bakarsu na zama tare dani a fada a matsayinsu na mata na. Wacce bata kai sauran ilimi a cikinsu ba ita ce mai Dufuloma na biyu, kuma yanzu haka tana jami'a. Bana cin zarafi ko wulakanta mata.

Kara karanta wannan

Abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Marigayi Sarkin Oyo, Alaafin Lamidi Adeyemi

"Kowacce abokiyar zama daga cikinsu tana da rawar da take takawa a aure. Kowacce daga cikin mata na tana da sashinta daban. Ubangiji ya bani wata irin baiwa da damar kula da mace, musamman kyawawan mata. Ba na fallasa hirarrakina ko wani abu da nayi da daya ga wata daga cikinsu. Ina da matsanancin rike sirri.
"Na koya bada gudunmawa mai kyau ga rayuwar mutane. Tabbas, su (mata) wani lokaci su na samun rashin fahimta ko rikici akan wani ra'ayi, amma, Ubangiji ya bani baiwar tabbatar da rikici bai yi kamari ba."

Limamin Kasar Oyo ya ja Sallar jana'izar Oba Lamidi Adeyemi

A wani labari na daban, babban Limani kasar Oyo, Sheikh Mas'ud Ajokidero, da dimbin jama'a sun yi wa marigayi Oba Lamidi Adeyemi Sallar jana'iza a fadarsa dake cikin jihar Oyo.

Hotunan da Legit ta samu daga wani Kehinde sun nuna lokacin da jama'ar garin ke kabarta Sallah kan gawar.

Kara karanta wannan

Sunaye da hotunan manyan sarakuna 3 da suka mutu a jihar Oyo cikin watanni biyar

Asali: Legit.ng

Online view pixel