Da Dumi-Dumi: Wasu yan bindiga sun turo sakon Bidiyo, sun yi barazanar hana zaɓen 2023

Da Dumi-Dumi: Wasu yan bindiga sun turo sakon Bidiyo, sun yi barazanar hana zaɓen 2023

  • Yan bindigan da suka addabi yankin kudu maso gabashin Najeriya sun saki wani sabon Bidiyon abin da suka kuduri aniya
  • A cikin gargaɗin da suka yi a Bidiyon, yan ta'addan sun yi barazanar hana zaɓen 2023 dake tafe a kudu maso gabas
  • A cewar su ba abin da zai dakatar da su har sai gwamnati ta sako shugaban yan awaren IPOB, Nnamdi Kanu

Wasu tsagerun yan bindiga da suka hana yankin kudu maso gabashin Najeriya zaman lafiya sun saki wani sabon bidiyo inda suka ayyan wasu abubuwan da suka sa a gaba.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa daga cikin manufofin su da suka bayyana, yan ta'adda sun yi barazanar hana zaɓen 2023 a baki ɗaya yankin kudu maso gabas.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Har yanzu ina shawarar takara, ku dakace ni: Goodluck Jonathan

Bidiyon mai tsawon mintuna biyu da dakika 55, wanda aka ɗauka a cikin ƙungurmin daji, ɗaya daga cikin yan bindigan ya ce abin da ya sa suka ja daga shi ne tsare shugaban yan awaren kafa ƙasar Biafara (IPOB), Nnamdi Kanu.

Yan bindiga sun saki sabon bidiyo.
Da Dumi-Dumi: Wasu yan bindiga sun turo sakon Bidiyo, sun yi barazanar hana zaɓen 2023 Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Haka nan kuma ɗan bindigan da ya yi maganan ya yi iƙirarin cewa babu wanda ke ɗaukar nauyin su, inda ya jaddada cewa, "Duk mutumin da ya jaraba yunkurin gudanar da zaɓe zai mutu."

Wane sako suka isar a sabon Bidiyon?

Rahotanni sun bayyana cewa yan ta'addan sun saki sabon Bidiyon ranar Alhamis, 21 ga watan Afrilu, 2022.

A cikin Bidiyon yan bindigan suka ce:

"Mu yan bindigan da ba'a sani ba a yankin ƙasar Biafara mun fito mu bayyana wa duniya matsayar da muka cimma wa. Mun shirya kare mahaifar mu ta kowane hali, ba bu wanda ke ɗaukar nauyin mu."

Kara karanta wannan

Komin rashin tsaro sai mun yi zaben 2023, Shugaban hukumar INEC

"Ba mu ƙarƙashin ikon Simon Ekpa, DOS ko kuma Uwazuruike, duk gwamnatin da take bai wa ɗaya daga cikin waɗan nan mutanen tana bata lokaci ne. Sakin Nnamdi Kanu ne kaɗai zai sa mu saurara."
"Dokar zaman gida ranar Litinin tana nan daram, ba abun da zai dakatar da mu har sai an sako Nnamdi Kanu, shugaban IPOB. Ba za'a yi zaɓe ba, duk wanda ya yi yunkurin kawo abin sa ya shafi zabe zai mutu."

A wani labarin kuma Gwamnatin Neja ta tabbatar Jirgin yaƙin Sojoji ya kashe kananan yara bisa kuskure

Gwamnatin jihar Neja ta tabbatar da kashe kananan yara shida a wani samame da jirgin yaƙin sojoji ya nufi yan ta'adda a jahar.

Sakataren gwamnatin jihar, Ibrahim Matane, ya ce tabbas lamarin ya faru kuma yanzu haka suna cigaba da bincike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262