Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Neja ta tabbatar da yawan kananan yaran da Jirgin yaƙin Sojoji ya kashe

Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Neja ta tabbatar da yawan kananan yaran da Jirgin yaƙin Sojoji ya kashe

  • Gwamnatin jihar Neja ta tabbatar da kashe kananan yara shida a wani samame da jirgin yaƙin sojoji ya nufi yan ta'adda a jahar
  • Sakataren gwamnatin jihar, Ibrahim Matane, ya ce tabbas lamarin ya faru kuma yanzu haka suna cigaba da bincike
  • Kananan yara shida ne suka rasa rayuwarsu a kan hanyarsu ta komawa gida daga wurin ɗebo ruwa a yankin

Niger - Sakataren gwamnatin jihar Neja, Ibrahim Matane, ya tabbatar da kashe kananan yara shida bisa kuskure wanda jirgin yaƙin sojin sama NAF ya yi a jihar.

Jaridar Punch ta rahoto Sakataren gwamnatin na cewa sun gudanar da bincike don tabbatar da lamarin wanda ya faru a makon da ya shuɗe.

Ya ce kananan yaran sun rasa rayuwarsu ne yayin da jirgin yaƙin ke aikin tarwatsa yan ta'adda a wasu sansanonin su dake cikin jihar.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yan Boko Haram 72 sun mika wuya ga Sojoji a Arewa maso gabas

Jirgin yaƙin Sojoji.
Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Neja ta tabbatar da yawan kananan yaran da Jirgin yaƙin Sojoji ya kashe Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton faruwar lamarin wanda ya auku a kauyen Kurebe dake ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Neja.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da aka tambaye shi, shin jirgin yakin NAF ne ya yi ajalin kananan yaran shida, Matane ya ce:

"Eh lamarin ya auki, gwamnatin Neja ta yi duba zuwa lamarin kuma tana cigaba da gudanar da bincike domin gano ainihin abun da ya faru."

Yadda lamarin ya faru

A cewar shugaban gamayyar ƙungiyoyin al'umma na Shiroro, Salis Sambo, jirgin yaƙin ya yi kuskuren kashe yaran ne lokacin da yake kokarin jefa wa wasu yan ta'adda Bam, waɗan da suka gudu cikin ƙauyen domin tsira.

Ya ce yaran da abun ya shafa suna kan hanyar su ta dawowa daga wurin debo ruwa, inda ya ƙara da cewa mutum hudu daga cikin su yan gida ɗaya ne.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya karyata Buhari baro-baro, ya ce an fi samun zaman lafiya a mulkin Jonathan

Ya ce:

"Yan ta'adda suka nufa da harin, a wannan makon Sojoji sun kaddamar da hare-hare hudu a Shiroro, sun samu nasarar halaka dandazon yan ta'adda."

A wani labarin kuma Farfesan wata Jami'ar Najeriya ya mutu awanni bayan kubuta daga hannun yan bindiga

Awanni bayan kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane wani Malamin Jami'a ya rasu a kan hanyar zuwa Asibiti.

Lakcaran mai suna, Farfesa Ovaborhene Idamoyibo, ya shiga hannun yan ta'adda ne ranar 9 ga watan Afrilu, suka sako shi ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel